Connect with us

RAHOTANNI

Akwai Bukatar WUDTOBA Ta Tabbatar Tana Tafiya Da Kowa A Cikinta –Bala Ibrahim

Published

on

Akwai bukakar kungiyar tsofaffun dalibai ta Wudil Technical Old Boys Association WUDTOBA a takaice ta tabbatar ta hada kan ‘ya ‘yanta ta hanyar tafiya da kowa-da kowa ta hanyar gayyatar kowanne tsohon dalibi da akayi karatu da shi a wannan lokaci dama tsohowar makarantar baki daya mekarfi da mara karfi maimukami da mara mukami domin tabbabatar da an hada karfi da karfe ta hanyar neman shawara da basirar kuwanne tsohun dalibi na’aga antemakawa makarantar da sauran makarantu na jahar Kano dama na wajen Kano da sauran masu tsananin taimako a cikin wannan kungiya dama sauran al’umma a Nijeriya.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Bala Ibrahim tsohon Ma’aikacin sashin Hausa na BBC LONDON member wato daya daga cikin ‘yan kungiyar ta WUDTOBA a lokacin da ya ke karin haske ga manaima labarai a lokacin taron kungiyar wanda aka gabatar a dakin karatu na Murtala Muhammad da ke Birnin Kano Dabo a ranar Lahadi da ta gabata.
Malam Bala Ibrahim BBC ya ce ya zama wajibi a duk lokacin da za’ai taron ayi amfani da kundin bayanai na kungiyar dana makarantar a tabbatar an zakulu kuwa da kuwa kada ayi la’akari da cewa sai mai mukami ku mai hali kuwa nada mahimman ci da kuma irin gudumuwar da zai bayar a wannan tafiya ta WUDTOBA.
Haka kuma ya kara da cewa wani abu ya fi birgeshi a wannan taro shi ne yadda ya ga cewa yau shekaru 40 da gama wannan makaranta gashi an hadu wasu daka cikin malamansu da wasu daga cikin daliban da suka halarci taron duk ana rayi wannan abun godiya ne da Allah madaukakin Sarki kuma abun farinciki ne kwarai da gaske a wannan rana.
Haka kuma a bunban tsoro shi ne kasancewarsu a da Yara, ne su yau kuma gashi wasu dayawa daga cikin su tsufa ya cimmusu batare da sanarwa ciwa zaizo ba kuma abun karfafa gwiwa shi ne yadda wasu suka zo da ‘ya ‘yan su wannan taro kuma wasu suka yi yunkurin zuwa da jikukin su wannan taro to wannan ya nuna cewa duk inda kaga tsoho to da yaro ne saboda haka a lamace ta cewa yaro zai zama tsoho kuma da dadadden ilimi ne da ya kamata al’umma ta rika la’akari da shi a kuyaushe.
Malam Bala Ibrahim haziki mai basira fitattce a aikin jarida ya bayyana cewa bayan barinsa sashin Hausa na BBC LONDON yanzu haka yana tare da shugaban rundinar ‘yan sandan Nijeriya ne a matsayin mai bashi shawara akan hurda da ‘yan jaridu da kuma al’umma wannan shi ne aikin sa na yanzu wanda yake dare da AIG Alhaji Ibrahim K. Idris shugaban rundinar ‘yan sandan Nijeriya.
Haka kuma a karshe ya bayyana cewa sun kai ne a ce tsofaffun dalibai makarantar su kawai zasu taimakawa a kwai bukatar a taimakawa makarantu na kusa da na nesa da kuma sauran al’umma gwargwadon hali a wannan lokaci a cewar Malam Bala Ibrahim BBC.
Shima daya daya daga cikin ‘yan kungiyar Alhaji Muhammad Bala Mai Turare ya bayyana cewa irin tarbiyar da aka musu inya tuna yana sa shi tunani mai zurfi da kuma gane cewa ashe kauna ce ta sa akai musu tarbiyya ba kiyayya ba don haka akwai bukatar irin rayuwar mutanen Dauri wato irin mutanen mu na da da su ke daukar kuwanne da, dansu ne kuma su masa tarbiyya yadda zata’amfani rayuwar sa agaba da sauran al’umma wanda irin wannan ce tasa duk da irin makudai kudin da yake biyawa dansa na makaranta a Abuja amma wata rana ya yanke shawara yakawu Dansa wannan makaranta ya ga yadda rayuwa ta ke kuma yazo ya gani ta zame mai darasi kuma tabashi karfin gwiwa ta hanyar samun wata tarbiyya data kai shi ga samun babban Digiri mai daraja ta daya a birnin London a cewar Alhaji Muhammad Bala Mai Turare tsohon Darakta a CBN.
Inda ya ce a kwai bukakar duk wanda ya ga yana ma danka tarbiyya tsakanin makuta, unguwa da gari da kasa to ka dauka kuma ka yarda a ranka cewa wannan masoyinka ne domin su gashi ya ga wannan inyatuna har kuka yake saboda dogun tunani a kan wannan babban al’amari da yafaru kuma ya amfani rayuwar su bayan makaranta.
Shi ma a nasa bangaren Babban Bako mai Jawabi Barista Sani Hussaini Garin Gabas SAN ya bayyana iri mahimmancin wannan taro da kuma fadi tashi na rayuwa har nasara ta samu a matsayin sa na dan wannan makaranta kuma wanda yake alfahari da ita don haka ya bayyaba cewa duk abin da mutum ya zama na daukaka a rayuwa to wannan makaranta itace tushi da za’ai alfahari da ita a kuda yaushe kamar yadda za’ai alfahari da iyaye da makarantar firamare da kuma irin tarbiyyar da aka samu da taimako na’iyaye da malamai a kuwanne mataki na rayuwa. Kuma ya bayyana cewa jajircewa da sa abu a arai da addu’a na daga cikin abubuwan da suke sa a cimma buri wanda hakan ce ta sa cikin yardar Allah ya kaiga mukamin SAN a matsayin sa na Lauya.
Shi ma shugaban kungiyar WUDTOBA Alhaji Abdulkadir ya bawa tsofaffin daliban yayi akan irin gudummawar da suke bayarwa na kungiyar da makarantar da suka kammala shekaru 40 da suka wuce ta Wudil Technical.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!