Connect with us

MANYAN LABARAI

An Cafke Direban Da A Ke Zargi Da Yi Wa ’Yar Shekara 78 Fyade A Legas

Published

on

A ranar Litinin ne, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Legas, Edgal Imohimi, ya shelanata kama wani direban motar haya bas, mai suna Jelili Lawal, wanda ake zargi da yi wa wata tsohuwa mai shekaru 78 fyade, a lokacin da ta bata hanya a Legas.
Wanda ake zargin mai shekaru 41, a ranar Litinin din ne rundunar ‘yan sandar ta nuna shi ga manema labarai a shalkwatar ta da ke Legas.
A cewar Kwamishinan ‘yan sandan, a ranar 1 ga watan Janiaru, 2019, da misalin karfe 200, wacce aka yi wa fyaden ta shaidawa Jilili, a daidai Mairyland, a can Legas cewa ta bace hanya, ta kasa gane hanyar komawa gidan su da ke Ketu.
Ya ce, sai Jelili Lawal, ya nuna zai taimaka mata, a kan hakan sai matar ta yi farin ciki da hakan, sai ta shiga motar na shi ba tare da sanin cewa Jilili yana da wani mummunan nufi ne da ita ba.
“Sai wanda ake tuhumar ya tuka motar da matar a ciki zuwa wani waje a kauyan Oloti, da ke wajen Adeniyi Jones Ikeja, ya yi mata fyade ba tare da la’akari da shekarunta ba.”
“A lokacin da yake yi mata fyaden ne, sai matar ta kwala ihun da ya janyo hankalin wani da ke da makwabtaka da wajen wanda ya hanzarta kiran ‘yan sanda, ya nuna masu wajen da kukan matan ke fitowa.
“Da hakan ne ‘yan sandan suka sami nasarar kama wanda ake tuhuman turmi da tabarya, wanda har ya rigaya ya ji mata ciwo jini yana zuba daga al’auranta a bisa dalilin keta mata alfarman da ya yi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce, an kai matar Asibiti, inda kwararru ke kokarin kwantar mata da hankali.
“A yanzun haka kuma ana shirin gabatar da wanda ake tuhuman ne a gaban kotu a kan abin da ya aikatan.”
Hakanan, a ranar 3 ga watan na Janairu, 2019, an yi karar wani mai suna Samuel Balogun, wanda ke zaune a gida mai lamba 17 a kan titin Ademola Abiola, Unguwar Alakuko, Legas, a ofishin ‘yan sanda da ke Alakuko, a kan cewa, ya dauki wata yarinya mai kimanin shekaru 12 zuwa wani kango da ba a kare ginin sa ba, ya kuma yi mata fyade.
“Inda a nan take ne aka kama Balogun Samuel, a yanzun haka yana kan bincike a sashen bincikar laifukan da aka aikatawa yara kanana na rundunar ‘yan sandan.
Imohimi ya ce, da zaran sun kammala bincike za su gabatar da wanda ake tuhuman a gaban kotu a bisa laifin keta alfarman karamar yarinya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!