Connect with us

MANYAN LABARAI

Boko Haram: Gwamnatin Borno Ta Gabatarwa Da Shugaba Buhari Bukatu 10

Published

on

A jiya ne, wata tawaga mai karfi da ta kunshi Sarakunan gargajiya, Shugabannin Addini, Kungiyoyin Mata da ‘Yan siyasa, a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, suka gabatarwa da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wasu bukatun su guda 10, a kan hanyar da za a bi a magance sake farfadowar ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, a Jihar.
Gwamna Shittima ya ce, bukatun sun samu ne a sakamakon la’akarin da taron da suka yi a kan sha’anin tsaron Jihar a Maiduguri a ranar Litinin ta makon da ya gabata ya haifar.
Duk da cewa, ba a bayyana abin da ke cikin wasikar da suka gabatar masa ba filla-filla, amma dai an ce ta kunshi matakai ne da tawagar take ganin in an yi aiki da su za su taimaka wa kokarin da ake yi na ganin an kawo karshen ‘yan ta’addan na Boko Haram.
Har’ila yau, a cikin tawagar akwai Dattawan Jihar, wakilan majalisun Jihar da na tarayya da suka fito daga Jihar, Shugabannin kananan hukumomin Jihar, Kungiyoyin mata, Kungiyar ‘yan Jaridu na Jihar da kungiyoyin kwadago, duk daga Jihar ta Borno.
Gwamna Shettima, a jawabinsa na bude zaman ya ce, abubuwan da aka yi la’akari da su din da kuma bukatun, ba a bayyanar da su ba saboda sun shafi lamarin tsaro ne.
Ya ce, “Mai Girma Shugaban Kasa, mun zo ne da wasu abubuwa da muka yi la’akari da su, da kuma wasu bukatun mu guda 10, domin neman hanzarta sa hannun gwamnatin tarayya a kansu. Duk wadannan abubuwan sun samu ne daga tattaunawar da muka yi a bayan taron sha’anin tsaron da mukan yi a mako guda da ya gabata.
“Ba mu yi gaggawan zuwa ne ba bayan taron namu. Sai muka ga dacewar mu ziyarci yankunan na arewacin Borno, mu tattauna da al’umman wajen da aka daidaita da kuma Sojojin da ke wajen domin karfafa wa tabbacin da al’umma ke da shi.
“Ina bukatar fahimtar juna daga manema labarai, da kar su yayata duk wani abu da muka tattauna a kansa na daga abin da muka yi la’akari da su da kuma wadannan bukatun namu guda 10. Abubuwa ne da suka shafi sha’anin tsaro, wadanda muke da nufin tattaunawa a kansu da Shugaban kasa a cikin sirri.”
Gwamnan ya bayyana cewa, al’umman Jihar Borno sun bayyana aniyar su ta yakan Boko Haram a sarari, ta hanyar bayar da gudummawar ‘ya’yansu a wajen yakar Boko Haram, a matsayin ‘yan sa kai na, Cibilian JTF.
Ya ce, tun daga 2013, sama da matasa 20,000 ‘yan sa kai, da suka hada da matasa ‘yan mata, duk sun sadaukar da kansu a wajen yaki da ‘yan Boko Haram, a karkashin tawagar ta, Cibilian JTF.
“Daga 2013 zuwa yanzun, Gwamnatin mu ce ke daukan nauyi daruruwan nasarorin da aka samu a farmakin da ‘yan tawagar na, Cibilian JTF, suka kai a kan ‘yan ta’addan na Boko Haram. Mu ke daukan su a aikin, bayan jami’an tsaro na DSS sun tantance su,” in ji Gwamnan.
Shettima ya ce, a tsakanin shekarun 2013 da 2014 ne muka sha wahala sosai a Jihar Borno.
“A daidai wannan lokacin, Boko Haram sun sace mana ‘ya’ya, sun kai farmaki masu yawa, har sun karbe ikon kananan hukumomi 20 daga cikin 27 da muke da su a Jihar Borno.
“A bangare guda kuma, a tsakanin 2015 zuwa 2018, Sojojin Nijeriya, tare da kai a matsayin babban Kwamanda, sun iya kwato dukkanin kananan hukumomi 20 wadanda a baya suke a karkashin ‘yan ta’addan na Boko Haram,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!