Connect with us

KASUWANCI

Gwamnati Za Ta Bunkasa Harkokin Tashar ‘Container’ Na Kaduna

Published

on

Mahukuntan kamfanin tashar ajiye kaya ta kan tudu dake cikin jihar Kaduna, sun bayyana crwar, rashin kyawun hanyar layin dogo da kuma hanyar ziga-zirgar motoci a daukacin fadin kasar nan yana zamowa kamfanin kalubale. In za’a iya tunawa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar ta kaduna a shekarar data gabata.
Acewar kafar yanar gizon hukumar tashar an sadata kai tsaye ne da layin dogo kai tsaye da kuma manyan hknyoyi a matsayin cibiyar safarar kaya daga tekunan kasar nan zuwa tashar. Manajan tashar, Mista Rotimi Raimi ne ya sanar da hakan a hirar sa da Jaridar Punch a Kaduna.
Ya ci gaba da cewa, kalubaken ya kara tsawwala kudin sufuri kaya daga tashar ruwa ta Legas zuwa tashar ta kan tudu. Rotimi Raimi ya kuma nuna damuwar sa a kan lamarin, inda ya ce, hakan yana janyowa tashar cikas wajen gudanar da ayyukan ta. Acewar Raimi, za’a iya magance matsalar ta tsawalla farashin na zirga-zirga ce idan hukumar sufurin jiragen kasa ta kasa ta samar da taragogin jiragen kasa da dama da kuma jiragen da zasu yi safarar kayan daga bakin teku zuwa tashar ta kan tudu.
Ya bayyana cewar, tashar ta Kaduna na bukatar ciyar da tattalin arzikin jihar da kuma yankin Arewacin Nijeriya baki daya. Ya yi nuni da cewar, abinda ke kara inganta tattalin arzijin jihar Legas shi ne filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala dake jihar ta Legas da kuma tashoshin jirgin ruwa dake cikin jihar. Ya yi nuni da cewar, ssboda samar da tashar ta tudu da kuma filin tashi da sukar jiragen sama a jihar Kaduna ya kamata ace ayyukan kasuwanci suna kankama kamar yadda ya dace, amma sai gashi tsadar ta tsawwala. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta samar kara samar da jiragen kasa da taragogi don gudanar da hada-hadar zirga-zirga kamar yadda akayi alkawari.
Ya sanar da cewar, wasu daga cikin dalilan da ya sanya kamfanonin tura kaya suke ja da baya da tashar sune, suna yun dubi ne a kan tsadar, inda ya buga misali da cewar, kamar ka biya kudin tashar da kuma na bakin teku, a tashar ta tudu zaka biya ta nata naira 150,000 kafin kwantainar ka ta sauka a tashar ta tudu ta Kaduna, inda zai iya kaiwa daga naira 600,000 zuwa naira 700,000, shin wanene zai biya sauran ?
Acewar sa, wannan shi ne kalubalen da muke fuskanta. Layin na dogo zai iya tura kwantainoni daga 20 zuwa 30 a lokaci daya, inda abinda ya kamata hukumar tashoshin jiragen kasa ya kamata ta yi shi ne ta tsara tashin jiragen don komai ayi shi a cijin sauki. In kaje kasar Afirka ta Kudu da sauran kasashrn da suka ci gaba suma haka suke yi.
Koda yake ya ce, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kara samar da jiragen kasa da taragugi a cikin wannan shekarar in har ta cika wannam alkwarin, zai rage matsalolin da ake fuskanta. Ya ce, har a yanzu muma yin amfani da hanyiyi ne. A karshe ya yi kira ga masu yin safarar kaya suyi amfani da tashar ta tudu wajen jigar kayan su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: