Connect with us

MAKALAR YAU

Rashin Tsaro: Wanne Gwamna Zai Sha Ta Dubu Ya Yi Irin Na Masari?

Published

on

Matsalar tsaro ko rashin tsaro shi ne babban al’amarin da ya dabaibaye Nijeriya wanda kullin ake neman mafita, wani lokaci ma sai ayi kamar an fidda rai saboda yadda ake tafka asarar rayuka kulin ba dare ba rana.
Wannan lamari yaki ci yaki cinyewa, kasar ta koma kamar sauran yaki, idan kuwa ana maganar harbe-harbe ta koma kamar kasar Siriya ko Iraki. Su kuma shuwagabanni cewa suke yi ana samun cigaba a wannan bangare, a ya yin da wasu ke ganin ko jaraba sa’a ma ba a fara ba.
Sannan a daidai lokacin da duniya baki daya ta tabbatar da rashin tsaro a tarayyar Nijeriya inda har wasu kasashen waje suka bada tabbacin taimakawa wajan ganin an kawo karshen wannan balahirar ta kashe-kashen jama’a babu gaira babu dalili.
Sai dai kuma a gefe daya hukumomi musamman na jami’an tsaro na cewa an ci nasara gagaruma akan masu tada kayar baya, har suna bada albishir da cewa nan da wani lokaci sun zama tarihi, aikin da har yanzu ake ganin wankin hula na neman kai su dare.
Ana cikin wannan tafiya ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude ya baki ya ce ya cikawa ‘yan Nijeriya da suka zabi shi alkawarin da ya dauka musamman samar da tsaro a wannan kasa ta Nijeriya lamarin da yanzu haka ya zama wani sashe mai zaman kanshi tsakanin ‘yan Nijeriya wajan tafka muhawara.
Wani lokaci idan akan zo akan maganar tsaro sai ka ji ana wawantar da hankalin ‘yan Nijeriya da cewa harkar tsaro wani bangare ne mai zaman kansa wanda bai zama wajibi ‘yan kasa su sani ba, alhali kuwa ‘yan kasar su ne kullin ake kacewa kuma gwamnati na cewa tana biyan kudin aiki.
To, amma magana ta gaskiya abubuwa da suke faruwa wanda babu wanda bai sani ba, sun yi karo da abubuwa da manyan jami’an tsaron Nijeriya ke gayawa shugaba Buhari da sauran ‘yan kasa.
Har ya zuwan yanzu, alkalumma sun kasa bayyana takamaimai asarar rayukan da aka yi daga shekarar 2013 zuwa 2018 wanda hakan yana nuni da cewa kullin sai an rasa rayuka kuma ana cewa an samu tsaro, abin tambaya anan wanne irin tsaro aka samu ba dai wanda ‘yan Nijeriya ke gani na yau da kullin ba?
Masana masu sharhi akan harkokin tsaro kullin suna bayyana cewa maganar gaskiya shine wannan gwamnati ta gaza wajan samar da tsaro manyan jami’an tsaro basa fadin gaskiyar lamari amma kullin ana siyasa da raina hankali jama’a da farfaganda da maganar tsaro.
A irin wannan gaba ce, gwamna jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi dogo nazari da tunani game da wannan batu da babu gaskiya acikinsa sannan kuma kullin yana karbar rahotan tsaro daga hannun jami’an tsaro abubuwan da yake gani abin babu kyau.
A karshe dai ya yanke shawarar ya tillar da kwallon mangaro ya huta da kuda, inda ya kira taron gaggawa kan harkar tsaro da masu ruwa da tsaki domin a lalubo hanyar da za a yi maganin wannan matsala.
Akwai jahohi da yawa da suke fama da matsalar da tafi wanda jihar Katsina ke fuskanta, amma dai har zuwa yau ba su daina yaudarar kansu da jama’ar da suke mulki ba wajan gaya masu cewa akwai tsaro ko kuma suna gab da kawo karshen matsalar tsaro amma a zahirin gaskiya karya ce kawai.
Ko ba komi gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya ciri tuta domin ya bayyanawa duniya halin da jihar Katsina take ciki, saboda haka yana neman mafita kowa ya bada tasa gudunmawa domin kawa karshen wannan bala’i.
Ko kafin wannan rana gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana karara cewa kulin safiya yana kashe kimanin naira miliyan biyu akan harkar tsaro to amma duk da cewa a baya an samu nasara bai hanashi ya kara fitowa ya bayyana cewa to yanzu fa ga abinda ke faruwa ba saboda haka kowa ya sani sannan kowa ya bada tasa gudunmawa wajan ganin wannan matsala ta zo karshe.
Wannan ya nuna a fili wasu gwamnoni suna sane da halin da jama’arsu suke ciki amma sai su yi kunne uwar shegu da bukatun jama’ar su fifita na su akan na jama’ar da suka zabesu saboda son duniya da rashin tabbas idan an kwanta dama.
Maganganun da gwamna Masari ya yi sun burge da yawan jama’a domin acewarsa wasu ko ba komi ya fadi gaskiya yanzu abinda ya rage shine jami’an tsaro su bayyana abubuwan da suka yi da kudadan da aka ba su, sannan su fadi abubuwan da suke hange a matsayin matsala garesu wanda ada ba su bayyana ba.
“Rahotan da na samu daga hannun daraktan hukumar SSS na Katsina yau, duk rahotannin da aka bani daga sauran hukumomin tsaron daya ne kawai ba na satar mutane ko fashi da makami ba ko kuma barayin shanu ba. Wannan ya nuna cewa jihar Katsina tana karkashin kawanyar barazanar tsaro ke nan” Masari ya jadada
Acewarsa babu wani zabi da ya rage illa a nemi mafita, saboda ana maganar mafita ne akan jama’ar jahar Katsina da kuma ita kanta jihar da kasa baki daya, wannan shi ne babban dalilin da ya tara jama’a a wannan wuri domin tattaunawa da fatan za a samu mafita.
“Yanzu maganar Satar jama’a domin neman kudin fansa, fashin da makami da barayin shanu sun zama ruwan dare gama duniya a wannan jiha ta Katsina, saboda haka dole kowanne daga cikinmu yasa abinda zai yi don ganin wannan abun ya kawo karshe” in ji Masari.
Ta wani bangaran kuma gwamna Aminu Bello Masari ya sha soka akan wannan wadannan kalamai na shi musamman daga jam’iyyar adwa ta PDP in da ta ce ai Masari ya gama zance abinda kawai ya rage shi ne ya yi murabus daga kujerar gwamna tunda ya kasa.
Shugaban jam’iyyar PDP kuma dan takarar Mataimakin gwamna a wannan zabe mai zuwa Katsina Honorabul Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Katsina inda ya ce ya zama dole gwamna Masari ya sauka wadanda za su iya tsare al’umma su hau.
Sai dai kuma jam’iyyar adawa ta PDP na ganin wannan kalamai na gwamna Masari kamar ya sukawa cikinsa wuka ne, domin a cewarsu tunda har gwamna zai fito fili ya bayyana haka to yanzu babu wanda yake da tabbacin yana da tsaro a jihar Katsina.
Saboda haka sai shugaban jam’iyyar kuma dan takarar gwamna a zabe mai zuwa ya yi kira da babar murya da cewa ya kamata gwamna Masari ya sauka kawai ba tare da bata wani lokacoi ba tundabya nuna ya gaza.
Ya kuma kara da cewa kwanan nan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin zabansa a jihar Akwai Ibom ya tabbatarwa da duniya cewa ya cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabansa a shekarar 2015.
Koma dai menene yanzu ya ragewa wadanda suke shugabancin al’umma amma kuma sun kasa gaya masu gaskiya al’amari kullin sai yaudarar su da cewa an samu tsaro alhali ba haka zance yake ba.
Sannan akwai bukatar shi kanshi shugaba Buhari ya yi sabon tunani game da wannan matsala ya daina sakin baki akan abinda duk duniya ta yi itifakin cewa wannan matsala akwaita, amma kulin mahukunta a Nijeriya suna cewa ba haka bane, ka wai wasu ne ke ruruta wannan matsala.
Haka kuma sauran gwamnoni da suke da irin wannan matsala da kuma wadanda suke da wanda tafi ta jihar Katsina lallai akwai bukatar su kira irin wannan taro na gaggawa domin lalubo hanyar da za a magance wannan matsala kasancewar zabe na kara karatowa, wanda idan haka ta cigaba da faruwa to ba a san abinda hakan zai haifar ba.
Idan kuma za a cigaba da yaudarar juna su ne su shuwagabannin suka kallon talakawa ayaba su kuma talakawa suna kallon su birai har zuwa lokacin zabe, ba za aji amsar daga gareni ba, amma idan lokaci ya yi anyi ga mai fili ga Doki…
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!