Connect with us

SIYASA

Sakataren Jam’iyyar PDP Na Jihar Kebbi Ya Koma APC

Published

on

Sakataren jam’iyyar PDP reshen jihar Kebbi ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC. Alhaji Muhammadu Sakaba ya tattara komatsensa tare da magoya bayansa ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya tarbi Sakaba wanda ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP a yau Laraba. Sakaba ya bayyana cewa; ya koma jam’iyyar APC ne saboda yarda da nagartar shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Atiku Baugudu na jihar Kebbi. Ya ce; sun nuna jajircewa wajen gudanar da ayyukan ci gaban kasa a tsawon mulkinsu.

Ya yi fatan ya ci gaba da goya musu baya tare da ba su gudummawarsa domin gani sun cimma nasara.

Sakaba ya yi alkawarin cewa; zai tattara kan dubban magoya bayansa domin tabbatar da sun zabi Buhari da Bagudu a zaben 2019 da za a yi. Ya ce za su tabbata sun taimaka musu wajen bunkasa sashen noma domin ya zama wata hanya ta samun kudin shiga ga kasarnan.

Da yake maida jawabi, Gwamnan Bagudu, ya jinjinawa Sakaba bisa goyon bayan da ya nuna ga gwamnatin Buhari.

A karshe Gwamnan ya yi kira ga al’umma a jihar da su yi koyi da Sakaba wajen ci gaban jiharsu baki daya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!