Connect with us

MANYAN LABARAI

Satar Mutane A Katsina: Mai Shari’a Mamman Nasir Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Published

on

• Labarin Yadda Ya Kubuta –Rundunar ’Yan Sanda

A shekaran jiya ne Hakimin Malumfashi, Galadiman Katsina, Mai Shari’a Mamman Nasir ya tsallake rijiya da baya, yayin da wasu mahara suka yi yunkurin sace shi.
Mamman Nasir, wanda tsohon shugaban kotun daukaka kara ne ta tarayya, ya kubuta zuwa gida ne ba tare da samun ko kwarzane ba, amma mai taimaka masa da ake kira da Aminu, barayin mutanan sun yi awon gaba da shi.
Lamarin ya auku ne a ranar ta Litinin da misalin karfe 9:30 na dare a tsakanin garin Gora da Yammama, da ke kan hanyar Dayi zuwa Malumfashi, a karamar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.
‘Yan bindigan sun tare hanyar ne inda suke bincikar ababen hawa domin neman wandanda za su sace.
Hakimin ya yi nasarar canza motar da yake a ciki ne cikin hanzari, amma mai taimaka masan bai samu nasarar yin hakan ba da sauri, hakan ya sanya barayin mutanan suka yi awon gaba da shi tare da wasu fasinjojin zuwa cikin dajin da ke kusa.
Wani mazaunin garin na Malumfashi, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwan lamarin, ya ce, jama’a suna ta tururuwa zuwa fadar Galadiman na Katsina domin jajantawa.
A cewar sa, daga baya Hakimin ya nemi al’umma da su barshi ya sami dan hutawa daga firgicin da yake ciki a kan lamarin.
Kakakin rundunar ‘Yan sandan Jihar, SP Gambo Isa ya yi bayanin yadda mai shari’ar ya tsallake rijiya da baya. Wanda a cewarsa, hakan ta faru ne bisa taimakon gaggawa da jami’ansu suka bayar.
Ya ce, da misalin karfe 9:00 na dare wasu ‘yan bindiga mutum 30 suka tare hanyar Gora-Dayi, wanda bai da nisa da shiingen duba ababen hawa da ‘yan sandan suka sa.
Ya ce; “Mai shari’ar ya fada wannan tarnaki ne yayin da yake tafiya tare da direbansa da wani ma’aikacinsa guda daya daga Katsina zuwa garinsu Malumfashi.
“Wannan ya sa a ka yi gaggawan sanar da jami’anmu, suka kuma gaggauta hallara a wurin da a ke kokarin aikata danyen aikin. Wannan ne ya tseratar da Mai shari’a, Mamman Nasir.”
“Har sai da suka zo kan motar Mai Shari’ar, suka fito da direbansa inda suka yi mishi fashi, sannan kuma suka tafi da mai taimaka masa, Aminu Lawal”, inji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!