Connect with us

RAHOTANNI

Shugabanni Da Makusantansu Za A Zarga Idan Abubuwa Suka Tabarbare

Published

on

Shugabanci ba karamin abu ba ne a cikin al’umma domin shuganni sune masu alhakin tabbatar da zaman lafiya, ci gaban kasa da walwalar al’umma.
Idan aka sami shuganni nagari, masu tsoron Allah, da hakuri a matakai daban daban kuma suka sami mashawarta nagari, akan sami saukin tafiyar da mulki tare da kaiwa da nasarori a kowane fanni da bangarorin rayuwar al’umma.
Sai dai kash! abun takaici a kasar mu Nijeriya harkokin mulki suna gamuwa da cikas saboda yadda masu mulki suka zama basa sauraron koke koken al’umma, kuma basa son a nuna masu gaskiya da gazawar su sai dai fadanci duk abin da sukayi a fito ta kafafen yada labarai ana godiya da bambadanci.
Amma a duk lokacin da aka nunawa shuganni inda ya kamata a gyara daga nan duk wanda ya fadi gaskiya to ya zama dan’adawa da makiyi a wajen shuganni da makusantan su harda magoya baya.
Dukkan shugaban da shi kullum fatan sa yaji an yaba shi, ana gwarzanta shi domin yana aiki ba tare da sauraron gazawa da raunin sa wajen mulki ba, tabbas yana tattare da matsalolin da za su kai shi da nadama a yayin da mulki ya kare.
Idan kana cikin shugabanni zababbu ko nadaddu to ku sani duk abin da ku ka yi wa jama’a hakkin sune ku yi masu wajen sauke nauyin da Allah ya dora maku ku yi adalci ga al’ummar ku domin shine kadai hanyar tsiran ku.
Duk aikin da kuke yi wa al’umma bada aljihunku ku ke yi ba, da dukiyar al’umma kuke yi wadanda suka zabe ku suka yi maku alfarma amma bayan kun hau mulki sai su zama abonkan gabar ku ba za ku sake sauraron su ba sai lokuttan zabe sun zo wanda kuma babban kuskure ne da ya jawa wasu bakin jini.
Idan shuganni suka yi duba ta hangen nesa tare da cire son zuciya da son a kurara su za su iya ganewa makusantan su, fadawa da yankanzagin su in har baza su iya fitowa su gaya masu gaskiya kome dacin ta, sai dai mai za su samu, tabbas ire iren wadannan ba abokan zama bane. Idan kuka lura zaku ga duk gwamnati da su ake domin babu abin da suka sa a gaba sai fifita muradun kai ba maslahar jama’a ba. Idan mulki ya kare ba kunya ba tsoro ko sannin ya kamata sai su bar ku domin fatan su gafiya tsira da na bakin ki.
Kira na ga duk shuganni a matakin karamar hukuma, jihohi da tarayya su saurari duk sukar da a ka yi masu wajen neman kawo gyara da kyakkyawar niyya za ta kai su ga cimma nasarori fiye da kullum jira suke a yabe su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!