Connect with us

SIYASA

‘Yan Sanda Sun Gargadi Masu Lalata Allunan Kamfe A Kuros Riba

Published

on

Jami’an tsaron ‘yan Sandan jihar Kuros Riba ta gargadi magoya bayan jam’iyyun APC da PDP akan da su kiyaye ka da su sake suna farfasa allunan kamfen din ‘yan takarar gwamnoni a fadin jihar.

Wannan gargadin ya fito ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yan Sandan DSP Irene Ugbo ya bayar a garin Kalaba a yau Laraba.

Wannan gargadi ya biyo bayan korafin da ‘yan takarar gwamnonin na kowacce jam’iyya suka shigar bisa zargin yadda wadansu bata gari suka lalata musu hutunansu na Kamfe da suka kafa a jikin Allunan a fadin jihar.

“Mun samu labarin cewa wadansu magoya bayan jam’iyyun siyasa a jiharnan suna bi suna yaga fostocin ‘yan takara, wanda wannan yana haifar da matsalar tsaro a jihar. Muna mai sanarwa da al’umma cewa; duk wanda aka kama ko aka sami wata kungiya da hannu wajen wannan aikin, zai fuskanci fushin hukuma.” Inji sanarwar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!