Connect with us

RAHOTANNI

2019 Za Mu Zabi Wanda Ya Damu Da Mu Ne Kawai A Nasarawa -Al’ummar Lafia da Obi

Published

on

Al’umman garin Dodoguru mazauna yankin raya kasa ta Jankwe da ke kararamar hukumar Obi, a Jihar Nasarawa, sun jaddadawa dan takarar kujerar Majalisar wakilai ta Tarayya Honorabul Joseph Haruna Kigbu, cewa bana ma suna nan a kan bakansu, shi za su sake zabe.
Kuma sau goma idan zai fito takara, to kuri’ansu mazansu da matansu tashi ce. Suka ce duk ‘yan siyasan Jihar Nasarawa babu na biyun shi, saboda yana da zuciyar taimakawa al’umman Jihar.
Saboda haka, a 2011 “Mun baka kuri’unmu ka lashe zabe, kuma tafiyar ka ba mu ji kunya ba, mun tabbatar da mun tura wakili na kwarai mai tausayin al’umma wanda ya san abin da yake yi. Ka kuma nuna mana halasci ka yi abin kirki mun gani.
Abubuwan alherin da ka kawo a mazabarka ta Lafia da Obi, abubuwa ne da idanu suka gani kuma kowa ya sheda ka taimaki yaranmu ka ba su aikin yi, ka kuma samar mana da abubuwan more rayuwa.
A kanka muka san dadin mulkin Dimokuradiyya. Haka ne ya sa a 2015 muka sake ba ka kuri’a ka ci zabe, amma aka murde karfi da yaji, aka dora mana wani daban ya je Majalisar Wakilai yana barci, In ji Steben Macel, wani Dattajon da ya samu garabasan tallafin aikin Tiyatan Ido kyauta.
Steben, ya kara da cewa; ba mu ga amfanin wannan wanda yake Majalisa ba, saboda babu aikin fari, bare na baki.
Shi ma Alhaji Shehu Sule, wani bawan Allah daga Lafia ya ce; da ma siyasa domin riba ake yin ta, kuma ribar siyasa a Duniya ne saboda haka mutum ya zabi mutumin kirki irin su Dakta Joseph Haruna Kigbu, wadanda suka damu da al’umma kuma suke taimaka wa al’umma shi ne.
Ya ce; Dakta Joseph Haruna Kigbu, ba ya kan kujeran mulki, amma ya sayi Tiranfoma na wutan lantarki ya sanya a tsakiyan garin Lafia a Unguwar Liman inda shekara da shekaru suna fama da Matsalar wuta, yanzu al’umman Unguwar suna amfana da arzikin Dakta Kigbu.
Ita ma Hajiya Aisha Matar Malam, ta ce, Dakta Kigbu, ya yi wa yarinyarta Tiyata kyauta, wanda aka gagara yi mata a Asibiti, sun je wani Asibiti an sanya masu kudi mai yawa, amma kwanaki Dakta Kigbu, ya yi mata kyauta a lokacin da ya yi aiki a fadar Sarkin Lafia.
Madam Merry ta ce; babu wanda nake kauna kamar Mahaifiyata, kuma tana fama da cuta a cikinta ba mu da kudi ga shi Daktan Talakawa ya yi mata Tiyata kyauta ya kuma ba mu magani Allah Ya saka masa.
Shi ma Mai Unguwa Ali, ya yi kira ga al’umman Jihar Nasarawa da su daina siyasan Addini ko kabilanci, su zabi mutumin kirki da yake taimaka wa al’umma.
Ya ce; Daktan Talakawa sama da shekara 19 yana yin wannan aikin kyauta, kuma babu bambanci. Ya kara da cewa, bai taba ganin mutumin da baya kyamar al’umma kamar Dakta Kigbu ba.
Duk girman damuwarka zai saurare ka, duk yanayin ka zai saurare ka, idan ya yi alkawari yana cikawa ba ya yaudaran jama’a.
Kuma shi ne saboda tausayi ya gyara gidan Makafi, ya gina dakuna uku da bayan gida. Ga Babban Masallacin Idi na garin Lafia, shi ne ya gina Bohol ake shan ruwa saboda cibiyar jama’a ne.
Malam Danjuma Abubakar, ya yi kira ga al’umman Lafia da Obi cewa, “Mu yi wa kanmu karatun ta natsu, mu zabi mutanan da suka damu da mu.” Ya kara da cewa, ka da mu kuskura mu kara yin zaben tumun dare irin wanda muka yi a zaben 2015, wanda ga shi yanzu muna kuka da hawaye.
Mu tabbata mun zabi ire-iren Dakta Joseph Haruna Kigbu, saboda su ke waiwayan mu ko suna mulki ko ba su mulki. Suna da abin da za su ba mu, kuma suna duba lafiyarmu. Kamar Daktan Talakawa, kwanaki ya yi aikin kiwon lafiya kyauta a garin Lafia, sama da mutum 4000 suka samu tallafi daga Tiyata zuwa magani. Ga shi ya sake yi a Dodoguru, ga shi kuma a Adogi,
Allah kadai Ya san adadin mutanen da za su samu lafiya.
Shi ma babban Jagoran yakin neman zaben Dakta Kigbu, Alhaji Ali Garkuwan Lafia ya ce; duk wannan abin da ake yi kadanne, sai ma an bude babban Asibitin Talakawa da Dakta Joseph Haruna Kigbu, yake ginawa, daga ko’ina jama’a za su amfana ba sai ma al’umman Jihar Nasarawa kadai ba.
Saboda wannan Asibitin an gina shi ne saboda Talakawa, shi ya sa aka kira shi da Asibitin Talakawa. Kuma kwararrun Likitoci kamar yadda kuke ganin su a nan, akwai sashen kula da marasa lafiya dabam-dabam.
Cutar da ke damun jama’a a ce sai an je Shika da ke Zariya ko Jos ko Abuja ko Kaduna, to insha Allahu sai dai a yi addu’a saboda an tanadar da kwararrun Likitoci da kuma kayan aiki.
Nan ba da dadewa ba ne za a bude wannan Asibitin, saboda mun ga jama’a na cikin halin kunci na rashin lafiya, kuma ba a samun isasshen magani a Asibitin Gwamnati.
Ya kara da cewa, Asibitin Gwamnati babu wajen kwanciya bare isasshen magani, saboda yanzu an kammala komai na Asibitin Talakawa ya rage a budewa a kuma fara aiki.
Komai zai zo da sauki saboda Daktan Talakawa, Joseph Haruna Kigbu, ya ce; za a samar da komai da sauki idan za ka biya Naira dubu daya a wani Asibitin, idan ka zo Asibitin Talakawa Naira dari za ka biya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!