Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Cafke Dan Shekara 25 Da Laifin Satar Mota A Neja

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wani mutum mai suna Nasiru Baladan dan shekara 25 a karamar hukumar Suleja cikin jihar sakamakon satar mota. An bayyana cewa, ‘yan sanda sun cafke wanda ake zargi ne a ranar 4 ga watan Junairun shekarar 2019 da mota kirar Toyota Camry mai lamba kamar haka, Nasarawa AKW 722 AA. Majiyarmu ta labarta mana cewa, shi wanda ake zargin ya amsa motar ne a cikin watan Disamba daga hannun Usman wanda yake garin Gwagwalada wanda ake zargin cewa ya saci motar ne daga hunnun Akwa Mallo wanda suke yanki daya da wanda ake zargin cewa an bashi motar ya sayar. Bala ya amince a kan cewa yana da hannu wajen saida motocin sata a lokuta da dama da su ka gabata. Ya bayyana cewa, “ Ina saida motar sata a yanki Suleja, Minna da kuma saura wurere, ya danganta da inda aka sato motar. Muna da abokan ciniki wadanda muke tallata musu a cikin fadin kasar nan. “Usman ne ya shigar da ni cikin wannan mummunar kasuwanci, ban yi tunanin cewa haramtacciyar kasuwanci ba ce har sai da na tsinci kaina a hannun ‘yan sanda.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Muhammad Abubakar ya bayyana cewa, rundunarsa ta amso motar da aka sace daga hannun wadanda ake zargi. Ya kara da cewa, za a mika su zuwa kotu idan an kammala bincike.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!