Connect with us

SIYASA

Atiku Ne Mafi Dacewar Shugabancin Nijeriya – Hon Dasuki

Published

on

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne mafi cancantar shugabancin al’ummar kasar nan a bisa ga yadda jam’iyyar APC ta kasa sauke nauyin da al’umma suka dora mata.
Dan Majalisar da ke wakiltar Mazabar Kebbe/Tambuwal A Majalisar Wakilai Hon. Abdussamad Dasuki wanda ke neman sake komawa majalisa a karo na biyu ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da yakin neman zaben ‘yan takarar Kananan Hukumomin Kebbe Da Tambuwal wanda aka gudanar a Jabo da ke a Karamar Hukumar Tambuwal a jiya.
“Mun marawa Buhari baya a 2015 da nufin zai samar da canji mai ma’ana da amfani ga al’ummar kasa amma a yau kowa shaida ne yadda Buhari ya kasa sauke nauyin da aka dora masa wanda hakan ya sa jama’a kuka da kokawa, yadda a yau kowa ke ji a jikinsa ya zama lallai mu zabi Atiku Abubakar.” Ya bayyana.
Hon. Dasuki wanda shine Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa A Majalisar Wakikai ya bayyana cewar al’umma na bukatar sauyin mulkin Buhari wanda baya ga karuwar tabarbarewar sha’anin tsaro haka ma fatara, talauci da karuwar rashin ayyukan yi sun addabi jama’a daga Arewa zuwa Kudu.
Ya ce, a matsayinsa na wakilin al’umma zai kara jajircewa wajen gudanar da ingantaccen wakilci nagari domin bunkasa jin dadi da kyautata rayuwar al’ummar mazabarsa bakidaya.
Tun da farko a jawabinsa shugaban yakin neman zaben Yammacin Sakkwato, Tsohon Mataimakin Gwamna Barista Mukhtari Shagari ya bayyana cewar wajibi ne jama’a su zabi dukkanin ‘yan takarar PDP daga sama har kasa bakidaya domin samun ci-gaba mai amfani.
“Ba wai mu zo Tambuwal domin yakin neman zabe ba ne domin abin kunya ne a ce mun zo Tambuwal yakin neman zabe illa mun zo ne domin gabatar da ‘yan takarar mu na Majalisar Dattawa Sanata Ibrahim Danbaba, da na Majalisar Wakilai Hon. Abdussamad Dasuki da Majalisar Dokoki ta Jiha na Tambuwal ta Gabas Mode Ladan Sanyinna da Tambuwal ta Yamma, Sule Hansti, da na Kebbe, Shu’aibu Umar kuma muna son ku basu cikakken goyon baya domin ‘yan takara ne nagari masu kima, dattako da mutunci.” In ji Shagari.
Tsohon Ministan na Ruwa ya bayyana cewar babu abin nunawa a Gwamnatin APC baya ga tabarbarewar al’amurra, rashin daukar shawara, rashin kyakkyawan shugabanci ta yadda matasa kuka, talakawa kuka, dalibai kuka, manoma kuka, mata kuka don haka Nijeriya na bukatar hazikin shugaba wanda zai kawar da matsalolin kasa da ‘yan kasa irin Atiku Abubakar.
A kasaitaccen taron irinsa na farko a yankin, Hon. Dasuki ya bayar da kyautar motoci hudu kirar Fijo 406 da mashin 93 ga ‘yan siyasar Kebbe/Tambuwal haka ma Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba ya bayar da naira miliyan hudu ga matasa, mata da dattawan Kebbe/Tambuwal domin karfafa ayyukan jam’iyyar PDP.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!