Connect with us

MANYAN LABARAI

Babban Sufeto Ya Nada Sabon Sakataren ‘Yan Sanda

Published

on

Babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ya nada Mataimakin Sufeton ‘Yan sanda na kasa, AIG Taiwo Lakanu, a matsayin sabon Sakataren rundunar ‘yan sandan na kasa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan na kasa, DCP Jimoh Moshood, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.
DCP Jimoh Moshood ya ce, nadin ya fara aiki ne nan take, a sabili da ritayan da abokin aikinsa, AIG Abdul Bube, ya yi a ranar 31 ga watan Disamba, 2018, bayan ya kwashe shekaru 35 yana aikin na dan sanda.
Mista Lakanu, wanda shi ne Mataimakin Sufeton ‘yan sanda na baya-bayan nan a shiyya ta 7 Abuja, yana da ilimin Digiri a kan halayyan al’umma da shari’a, wanda ya samu daga Jami’ar Legas, da kuma digiri na biyu a kan ilimin shari’a, wanda ya samu daga Jami’ar Leeds Metropolitan Unibersity, Leeds, ta kasar Ingila.
Sabon Sakataren rundunar ‘yan sandan ya halarci kwasa-kwasai masu yawa a ciki da wajen kasar nan, da suka hada da kwas din bincikar masu laifi, ‘Crime Inbestigation Course,’ a Kwalejin ‘yan sanda da ke, Jos, da sauran su.
Ya yi aiki a bisa mukamai masu yawa na rundunar, ya yi aiki a matsayin, ‘AIG Federal Operations, a shalkwatar rundunar ‘yan sandan, Kwamishinan ‘yan sanda a Jihohin Imo da Ekiti, Kwamishinan ‘Yan sanda a sashen rundunar da ke filin saukan Jiragen sama na, Lagos, babban Jami’i a ofishin sufeton ‘yan sanda na kasa, (a shalkwatar rundunar ta shiyyar, Lagos) da sauran su.
Tuni dai Mista Lakanu, ya kama aiki a matsayin Sakataren rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!