Connect with us

SIYASA

Kaddamar Da Yakin Neman Zabe: ‘Yan Takarar Kujerar Gwamna 11 Sun Sauya Sheka A Adamawa

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na Adams Oshiomole, ya amshi ‘yan takarar kujerar gwamna goma sha daya da jam’yyunsu, da suka koma jam’iyyar APC a bukin kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar a jihar Adamawa.
Da yake jawabi a taron kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla, shugaban jam’iyyar APC na kasa shekaru uku da rabin da jam’iyyar tayi, ya fi shekaru goma sha shida da jam’iyyar PDP ta yi tana mulkin kasar.
Adams Oshiomole, ya ci gaba da cewa kuma jam’iyyar da dan takaranta shugaba Muhammadu Buhari, za ta ci gaba da yiwa kasar ayyuka musamman ta fannin gyara hanyoyin, Kiwon lafiya, tsaro da bunkasa tattalin arzikin kasar.
Ya ce “kada ku yarda ku bar Najeriya da ta koma hanun barayi, sun sace kudadenku kuma sun dawo sunason ku sace zabensu, kada ku amince da haka” inji Oshomole.
Da yake magana game da ‘yan takaran da suka Sauya shekar kuwa shugaban jam’iyyar ya yaba da jam’iyyu da suka ajiye bukatarsu ta tsayawa takara suka goyi bayan dan takaran jam’iyyar ya ce zasu aiki tare domin tabbatar da nasaran APC a zaben dake tafe.
Da shima ke jawabi a taron shugaban kungiyar yakin neman zaben APC kuma ministan ma’aikatar sufuri ta kasa Rotimi Amaechi, ya ce baya ga ayyukan hanyoyin da gwamnatin tarayya ta gida, ya ce gwamnatin na kuma shirin gina hanyar dogo da zai hada birnin tarayya Abuja zuwa Maiduguri zuwa Yola.
Ya ce “muddin ‘yan Nijeriya suka sake zaben shugaba Muhammadu Buhari akaro na biyu, zasu samu canji a rayuwarsu ba kawai ta fuskar ingantattun hanyoyi ba, harma da harkokin ci gaban rayuwarsu ta yau da kullum” inji Ameche.
Da shima ke jawabin amsar tutar tsayawa takarar kujerar, gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla, ya ce su a yankin arewa maso gabas akwai dalilai da dama da zasu sake zaben shugaba Buhari a karo na biyu.
Ya ce “kafin zuwan wannan gwamnati muna cikin tashin hankali, yanzu muna kwana idonmu rufe mu yi bacci iyasonmu, saboda haka zamu tabbatar mun dawoda shugaba Buhari, kan kujera a babban zabe mai zuwa.
“ina rokonku duk wanda bai amshi katin kada kuri’a ba, ya hanzarta amsa, saboda har yanzu INEC bata rufe bada katin zabe ba” inji Bindow.
Da shima ke jawabi tun da farko shugaban jam’iyyar APC a jihar Ibrahim Bilal, ya yiwa mahalarta taron maraba, ya ce jam’iyyar APC tayi rawar gani, ya ce idan jama’a kasar sake bata dama ba zata basu kunya ba.
Da yake magana amadadin ‘yan takaran kujerun gwamnan da suka Sauya shekar dan takaran gwamna karkashin jam’iyyar ANP Umar Cakulete, ya ce ganin ayyukan raya ci gaban jihar da gwamnan ke yi yasasu maramishi baya.
Jam’iyyyun da ‘yan takaransu suka Sauya shekar sun hada da Alliance For Party,ANP, PPN, KAP, JNPP, Kowa party,PPA ,ZLP, Young People Party,YPP,NAtional Conscience Party,WPP da kuma MEGA party.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!