Connect with us

KASUWANCI

Kayan Da Ake Shigowa Da Su Nijeriya Sun Lashe Naira Biliyan 837 A Watanni 11

Published

on

Sakamakon sanar da isassun kudin musaya na kasar waje da aka yi, hakan ya sanya masu sarrafa kaya a Nijeriya sun kashe kudi da yawa wajen shigo da kayan, inda kuma hakan ya janyo ruguwar kayan da ake samu a cijin Nijeriya a 2018, Anna Okon ya yi shirhi a kan hakan, ina Abubakar Abba ya fassara shirhin. Kayan na cikin gida da ake samowa, sun ragu matuka tun lokacin da Nijeriya ta auka a cikin ukubar matsin tattalin arzikin kasa, inda kuma masu sarrafawar suka bazama wajen neman kudin musaya na kasar waje. Kungiyar masana’antu ta kasa MAN, ta tabbatar da hakan a cikin hasashen ta data yi a kan kasafin kudin 2019.Shugaban kungiyar ta MAN, Mansur Ahmed ya ce, yawan samo kayan na cikin gida na fannin masana’antu ya ragu da kumanin kashi 57.87 bisa dari a 2018 daga kashi 63.21 bisa dari da aka samu a 2017. Har ila yau, a bisa bayanan da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta wallafa a Disambar 2018 ya nuna cewar, yawan kayan da aka shigo dasu a Janairu da Nuwambar 2018, sun kai na naira biliyan 837.5. Fashin bakin da aka yi na adadin, ya kai naira biliyan 284.81 na ywan kayan da aka shigo dasu ia farkon zangon shekarar, inda suka kai naira biliyan 261.10 a cikin zangon shekara ta biyu da kuma naira biliyan 291.57 a cikin zangon na biyu. Kayan da aka shigo dasu a zango na farko, sun kai kashi 1.93 bisa dari na karuwar su sama da yawan na zango hudu na 2017, wanda ya kai naira biliyan 279.41 da kuma samun karin da ya kai kashi 9.89 bisa dari sama da adadin naira biliyan 259.17 da aka samu a farkon zango na shekarar. Bugu kari, yawan kayan da aka shigo dasu a zango na biyu suna cewar sun ragu da kashi 8.3 bisa dari sama da yawan kayan da aka shigo dasu a zango na farko da kashi 14.2 bisa dari kasa da yawan kayan da aka shigo dasu a zangon 2017, wanda ya kai naira biliyan 304.43. Kayan da kuma aka shigo dasu a zango na uku, sun kai kashi 11.67 bisa dari sama da yawan kayan da aka shigo dasu zango na biyu da kuma kashi 2.19 bisa dari na sama da yawan kayan da aka shigo dasu a zango na farko. Abewar NBS, yawan kayan da aka sarrafa aka shigo dasu a farkon zangon 2018, sun kai naira tiriliyan1.19, inda suka ragu da kashi1.65 bisa dari na sama da zangon da ya gabata, wanda ya kai naira tiriliyan1.20, amma da karin kashi 12.11 bisa dari na sama da zangon 2017, wanda ya kai naira tiriliyan 1.061. Har ila yau, kashi 21.1 bisa dari na kayan da aka shigo dasu sunzo ne daga kasar China, inda suke da kashi 12.1 bisa dari, inda kuma na kasar na kasar Netherlands da kasar Belgium nasu ya kai kashi 10.6 bisa zari. Bugu da kari, kasar Amurka tana da kashi 6.5 bisa dar, inda kasar Indiya keda kashi 6.3 bisa dari. Bayan fitar da akayi daga cikin matsin tattalin arzikin kasa a 2016 da kuma ragewa dala karfi da Babban Bankin Nijeriya CBN ya yi da kuma kafa takunkumi a kan shigoda kaya kala 41 ta hanayar samo kudin musaya na kasar waje, masu mana’antu a Nijeriya sun bazama wajen samo kayan cikin gidada kuma kara jan damara. Kungiyar ta MAN ta ruwaito cewar sakamakon wanzar da tsarin ssmo kayan masana’antun na cikin gida gwamnatin tarayya ta yi, ya kara kayan zuwa kashi 65.7 bisa dari a 2017 daga kashi 59.98 bisa dari da aka samu a farkon rabin zango of 2016. Bugu da kari rungumar shirin sake jan damara da, ya samarwa da masana’antun damar kafa wurare na samo nasu kayan na cikin gida ya taimakawa manyan masana’antun da kuma sarrafa kayan na cikin gida da suke bukatar yin amfani dasu a masana’antun su. Haka yin amfani da kayan na cikin gida ya karu. Sai dai, abin takaici yan samo kayan na cikin gida sun ragu da kashi 5.34 bisa dari a zango na uku na 2018,inda kuma 54.6 bisa dari kuma kula dasu ya kai daga kashi 57.14 bisa dari da aka samu a 2017. Masanin tattalin arzikin kasa The dake a kungiyar ta MAN, Mista Ambrose Oruche, shima ya tabbatar da raguwar samo kayan na cikin gida saboda masu masana’antun, suna shigo dasu daga kasar waje fiye da yadda ake samo kayan na cijin gida. Da aka tambaye cewar kamar hakan ana yiwa kayan na cikin gida nakasu ne da kuma dauka ka darajar su Oruche ya ce, samo kayan na cikin gida masana’antun sunfi mayar da hankali ne a kan yadda zasu gyra madatsan su, inda hakan ya sanya suke shigo da kayan don su samu riba mai yawa. Ya ce, amma muna da shiri a wannan shekarar muna da tsari da zai.sada da kananan masana’antu da kuma manya don samo kayan na cimin gida. Fitar da kayan ya ragu da kashi 13.62 bisa daria farkon zangon 2018, inda aka samu naira biliyan 32.70 idsn aka kwatanta da zango na hudu na 2017 da ake da naira biliyan 37.85 amma an samu karin kashi 47.71 bisa dari idan aa kwatanta da farkin zangon 2017 da aka samu naira biliyan 22.13. Fitar da kayan ya ragu da kashi 2.98 bisa dari a zango na biyu the na 2018, inda aka samu naira biliyan 31.72 idan aka kwatanta da zangon farko, wanda keda naira biliyan 32.70, amma an samu karin kashi 19.7 bisa dari idan aka kwatanta da zango na biyu na 2017 da aka samu naira biliyan 26.50. Kayan da aka ssrrafa aka fitar dasu a zango na biyu na 2018 sun kai naira biliyan 69.86, inda suka nuna sun ragu da kashi 83.9 bisa dari sama da na zangon da ya gabata da aka samu naira biliyan 434.37 da kuma karin kashi 0.9 bisa dari idsn aka kwatanta da zango na biyu na 2017 wanda ya kai naira biliyan hich 69.26. A cikin zango na uku, kayan da aka fitar dasu sun karu da kashi 1.63 bisa dari , sama da yawan na zango na biyu dake da kashi 21.7 bisa dari, sama da yawan wanda aka samu a zango na uku na 2017.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!