Connect with us

LABARAI

Kungiyar ICRP Sun Fadakar Da Al’umma Kan Muhimmancin Kare ‘Yancin Bil’adama

Published

on

A yau Alhamis ne, 10 ga watan Janairun 2019, Kungiyar Sulhuntawa da kare Hakkin Bil’adama wacce aka fi sani da ICRP a turance, ta gudanar da wani taro da ya shafi kare hakkin Bil’adama a birnin Tarayya Abuja. Taron ya gudana ne a dakin taro na Otel din Savanneh Suites dake Area 3 a Abuja. Inda Malaman Jami’a, Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama, Dalibai, da sauran su suka halarci taron. Daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da; Farfesa Dahiru Yahaya daga BUK, Farfesa Abdullahi Danladi daga ABU, Ndi Kato mai rajin kare hakkin Bil’adama, Kwamared Musa da dai sauran su.

Shugaban Kungiyar, Kwamared Shu’aib Isa Ahmed, ya bayyana cewa; “Manufar wannan taron shi ne, domin mu zo mu hada kawukanmu a matsayinmu na ‘yan Nijeriya tare da kuma tattaunawa makomar kasarmu.” Ya ci gaba da cewa; “Yanzu komai ya tabarbare a Nijeriya, wanda ya hada da bangaren tattalin arziki, tsaro, take hakkin bil’adama, da kuma rashin bin doka da oda daga hukumomi da sauran su.” Inji shi.

Sai dai ya tabbatar da cewa; ya kamata a ce ‘yan Nijeriya sun fahimci cewa muna da bambanci a tsakaninmu, amma dole ne mu zauna tare. Ya nuna takaicinsa na yadda a da bamu rigingimu a tsakanin Musulmi da Kirista a kasarnan; “Amma yanzu mene ne yasa ake samun wadannan rigingimu? Rashin girmama fahimtar juna. Manufarmu shi ne tabbatar da Nijeriyar da kowa zai yi alfahari da ita. So muke mu hada kan al’umma, mu rika tunatar da al’umma muhimmancin zaman lafiya, sannan mu rika goyon bayan wadanda ake zalunta ba tare da la’akari da addininka ko kabilarka.” Inji Kwamared Shu’aib.

Da yake nasa jawabinsa, babban mai jawabi a wurin taron, Farfesa Dahiru Yahaya ya bayyana cewa; babbar matsalar da ake fuskanta a kasarnan shi ne; “Kasar ta fara zama kamar babu shugabanci.” Ya ce; domin yanzu an koma sam hukumomi basa bin doka da oda. Ya kara da cewa; babban abin takaicin shi ne, kowa ya san da wannan, amma kowa bai damu ba, hakazalika ma shuwagabannin ma suna nuna halin ko in kula.

Da yake magana dangane da tabarbarewar tsaron a kasarnan, ya ce; matsalar rashin tsaro ya faro daga Maiduguri tun zamanin tsohon shugaban kasa Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, ya ce yanzu abin ya dawo arewa maso yamma na kasarnan.

Ya nusasshe da yadda cewa; jami’an Soji ya kamata su zama ayyukansu na kare kasa ne, ba na cutar da al’umma ba. Ya kara da cewa; hakazalika ya kamata jami’an tsaron ‘yan Sanda su zama abokan ‘yan kasa ne. Ya nuna muhimmanci gwamnati ta rika sauraren al’umma, domin a cewarsa; karfi ba ya maganin komai. Ya shawarci shuwagabannin kasarnan da su zama suna fahimtar al’amura kafin su rika daukar matakai a kan su. Ya lurantar da mahalarta taron yadda tabarbarewar tsaro yake da da karuwa a kasarnan. Ya ce; “Da a arewa maso gabas ne, yanzu yana aukuwa a arewa maso yamma.” Ya nuna yadda kafin ‘yancin kan kasarnan da bayan ‘yancin kai, yadda kasar ake zaune lafiya a tsakanin mabiya addinai. Ya ce; shi yana ganin abubuwan da suka haifar da matsaloli a tsakanin addinai, shi ne yadda aka rika kawo fahimtoci daban-daban daga wajen kasarnan.

Ndi Kato, Kwamared Musa da Farfesa Abdullahi Danladi duk suna cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wurin taron. An fara lafiya an kare lafiya.

Kungiyar sun bayyana Kanal Sambo Dasuki, Shaikh Ibraheem Zakzaky, Zeenatuddeen Ibrahim da Kwamared Deji Adeyanju a matsayin wadanda gwamnati ke ci gaba da rike su ba bisa ka’ida ba duk da kuwa akwai umurnin kotu na cewa a sake su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!