Connect with us

WASANNI

Manchester United Za Ta Kashe Fam Miliyan 100 A Watan Janairu

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ware kudi kusan fam miliyan 100 domin siyan sababbin ‘yan wasa a watan Janairu nan da ake ciki domin kara karfi
Tun a farkon fara kakar wasa ne dai kungiyar taso ta siyi dan wasan baya sai dai shugabannin kungiyar basu bawa tsohon kociyan kungiyar Jose Mourinho damar siyan dan wasan na baya ba saboda dalilinsu na rashin tabbas a kasuwar.
A kwanakin baya dai tsohon kociyan Mourinho ya bayyana cewa akwai matsala a wannan kakar idan har kungiyar bata iya siyan dan wasan baya ba mai kyau domin bai yarda da wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar ba na baya.
Manchester United dai tana zawarcin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Fiorantina, Milenkobic da kuma dan wasan baya shima na kungiyar Roma, Monalos wanda akayiwa kudi fam miliyan 34.
Sai dai tuni kungiyar ta kori Mourinho kuma ta maye gurbinsa da tsohon dan wasan kungiyar Ole Gunnar Solkjaer wanda kawo yanzu yake saran kungiyar za ta siyo masa dan wasan baya.
A wasa na gaba dai Manchester United za ta kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a gasar firimiya kuma kungiyar yanzu itace a matsayi na shida akan teburin gasar ta bana yayinda Tottenham take mataki na 8
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!