Connect with us

KASUWANCI

NEXIM Ta Ware Naira Biliyan 36 Don Bukasa Jihohin Arewa

Published

on

Bankin dake fitar da kaya zuwa kasar waje na kasa NEXIM ya sanar da cewar, ya ware a kalla naira biliyan daya ga ko wacce jihohi 36 dake kasar nan don su samu damar ciyar da daya ko biyu na kayan su da basu shafi fannin mai ba, inda kudin suka kai jimlar naira biliyan 36. Manajin Daraktan Bankin NEXIM, Alhaji Abba Bello ne ya sanar da hakan a ranar litinin data wuce a jihar Katsina a taron kwana biyu da Bankin ya gudanar na wayar da kan yankin Areea maso Yamma a kan fitar da kayan zuwa kasar waje daga Nijeriya zuwa kasar waje. Alhaji Abba Bello ya ce, tallafin anyi shi ne a karkashin Gidauniyar Bankin na jiha da shiyya na fitar da kayan da nufin ciyar da fitar da kayan da basu shafi fannin mai ba zuwa kasar waje harda amfanin gona. Ya ci gaba da cewa, don cimma kudurin Bankin na samar da tsare-tsare da daukaka darajar masana’antun dake yankin Arewacin kasar nan, wajen fitar da kayan zuwa waje da kuma daukaka darajar matsakaitan sana’oi, musamman yadda zasu shiga kasuwannin duniya, Bankin ya kaddamar da sabon tsari da ake kira PABE, na fitar da kayan zuwa waje don su kara yin daraja, inda ya yi nuni da cewar, shirin zai juma samar da sauki wajen fitar da kayan zuwa waje, samar da ayyukan yi da kuma kara samar da kudin shiga. Manajin Daraktan ya kara da cewa, don daukaka shirin na PAVE, Bankin ya gabatar da Gidauniyar ta jiha da shiyya ta ciyar da kayan da za’a fitar zuwa waje gaba, inda a kalla Bankin ya ware naira biliyan daya ga ko wacce jiha 36 don ciyar da kayan su da basu shafi fannin mai ba a gaba. Abba Bello a karshe ya ce, Bankin ya kuma ware kudin don tallafawa masana’antu ganin cewar sune manya wajen samar da ayyuka yi ga yan Nijeriya mata da matasa a karkashin shiri na musamman na na ragr talauci ga marasa galihu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!