Connect with us

SIYASA

Osinbajo Ya Shawarci ‘Yan Nijeriya Da Su Yi Aiki Tukuru Wajen Ci Gaban Dimokuradiyya

Published

on

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya roki ‘yan Nijeriya da su yi aiki tukuru wajen ganin an samu hadin kan al’umma da ci gaban dimokradiyya a kasarnan.

Osinbajo ya yi wannan kiran ne a yau Alhamis a St. Stephen’s Anglican Cathedral, dake Oke Aluko a jihar Ondo a lokacin bikin bizne gawar Marigayi Dk. Frederick Fasehun, wanda ya kirkiri Kungiyar Yarbawa ta OPC.

Da yake magana dangane da wanda ya rasu, ya bayyana cewa; ya gudanar da rayuwarsa ne da dukiyarsa wajen ganin ci gaban Dimokradiyya a Nijeriya ta hanyar amfani da kungiyarsa ta OPC da abin da ya faru a ranar 12 ga watan Yuni.

A karshe ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daga cikin wadanda suka kasance a wurin taron sun hada da; Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti sai tsohon gwamnan Ondo, Dk. Olusegun Mimiko, sannan sai karamin Ministan jihar Neja Delta, Farfesa Claudius Daramola, tare da dimbin Sarakunan gargajiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!