Connect with us

WASANNI

Real Madrd Za Ta Kashe Fam Miliyan 500 Domin Yin Garambawul

Published

on

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya kashe kudi kusan fam miliyan 500 domin siyan sababbin ‘yan wasa a kokarin da kungiyar take na yin garanbawul a sakamakon rashin kokari da kungiyar take a wannan kakar.
Real Madrid dai ta tsinci kanta a matsayi na biyar a gasar laligar kasar sipaniya sai dai kuma ba’ayi waje da ita ba a gasar cin kofin Copa Del Rey yayinda gasar zakarun turai kungiyar har yanzu tana bugawa kuma take saran za ta iya buga abin arziki.
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Harry Kane, Dan kasar ingila da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazardn wasa Erikson na Tottenham duk kungiyar take saran dauka a karshen kakar wasa.
Har ila yau kungiyar tana son ganin ta lallami kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta siyar mata da Neymar sannan kuma tana zawarcin dan wasan kungiyar Jubentus, Paulo Dybala dan kasar Argentina.
Real Madrid ta kammala daukar dan wasa Brahim Diaz daga kungiyar Manchester City akan yarjejeniyar sama da shekara shida kuma dan wasan zai fara bugawa kungiyar wasa kai tsaye.
Kuma Real Madrid ta gabatar da shi gaban magoya bayanta, inda Diaz ya yi godiya da tarbar da aka yi masa, sannan ya buga kwallaye cikin ‘yan kallo cikin farin ciki kuma kawo yanzu tuni yafara daukar horo da ragowar ‘yan wasan kungiyar.
Shugaban kungiyar, Florentino Perez ya bayyana cewa kungiyar ta shirya tsaf domin siyan manyan ‘yan wasa tunda daman ansan kungiyar da siyan manyan ‘yan wasa a duniya kuma babu wani dan wasa da zai yiwa kungiyar tsada idan har tana bukatarsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!