Connect with us

MANYAN LABARAI

Sojoji Sun Yi Babban Kamu A Nasarawa, Binuwai Da Taraba

Published

on

Sojojin Nijeriya dake aiki a karkashin shirin ‘Operation Wild Stroke’ a jihohin Nasarawa da Benuwai da kuma Taraba sun bayyana kashe ‘yan ta’adda 17 tare da kama wasu 67 a cikin wata 8 da suka yi suna aiki a jihohin.
Kwamanda shirin, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya sanar da haka a tattaunawarsa da ‘yan jarida jiya Laraba a garin Lafiya.
Kwamandan ya kuma gabatar da makamai 45 daban daban da albarushai 701 da aka kama a hannun ‘yan ta’adda a garin Bass, da kuma sansaninsu na Zwere, a karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa.
Ya kuma kara da cewa, rundunar ba za su huta ba har sai sun kakkabe ‘yan ta’adda a dukkan bangarorin jihohin guda uku.
Daga nan ya kuma ce, dakarun sun kashe ‘yan ta’adda 16 sun kuma kama mutum 53 tare da makamai 11 da albarushai 50 a jihar Benuwai.
“A jihar Nasarawa kuma an cafke makamai 48 da albarushai 801 an kuma cafke mutum 9 tare da kashe dan ta’adda daya.
“A jihar Taraba kuma Dakarunmu sun kwato makamai 7 da albarushai 35 an kuma samu nasarar kama mutum biyar tare da kashe dan ta’adda daya.
“Cikkaken bayanin dake a hannun mu na aikace aikacenmu ya nuna cewa, an kwato makamai 886 an kuma cafke mutum 67 an kuma samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 17 a yankin gaba daya,” inji shi.
Ya kuma kara da cewa, an kafa shirin na ‘Operation Wild Stroke’ a wata 8 da suka wuce da nufin kawo karshen kashe kashen da ke aukuwa tsakanin makiyaya da manoma tare da kuma kakkabe ‘yan ta’adda a yankin jihohin uku gaba daya,” inji shi.
Kammanda ya kuma tabbtar wa da jama’ar jihohin kudurin jamai’an tsaron na kawo karshen garkuwa da mutane da rikice rikicen dake aukuwa a tsakanin al’ummu a jihohin.
Ya kuma bukaci jama’ar jihohin su taimaka waje sanar da jami’an tsaro bayan harkokin ‘yan ta’adda don a kawar da su. Idan za a iya tunawa an samu rikici a tsakanin kabilun Bassa da Egbura dake karamar hukumar Toto a shekarar 2018 abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!