Connect with us

MANYAN LABARAI

’Yan Sanda Sun Tarwatsa Taron PDP A Jihar Jigawa

Published

on

Rundunar ‘Yan Sanda reshen jihar Jigawa ta yi amfani da sinadarin barkonon tsohuwa yadda ta tarwatsa dubban magoya bayan jam’iyyar adawa ta PDP a lokacin da suke gudanar da taronsu a Jigawa.
Taron wadda aka shirya yinsa a jiya a garin Gumel an shirya shine domin kaddamar da fara kamfen da kuma baiwa ‘yan takara dake yankin Arewa maso gabas na jihar tuta ya sami tangarda daga rundunar ‘Yan Sanda wadda ake zargin hakan ta faru sakamakon kin bin umarnin ‘Yan Sandan na sauya ranar taron.
Shi kuwa da yake bayyana damuwarsa kan wannan al’amari, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP yankin Arewa maso gabas a jihar Alhaji Babandi Ibrahim Gumel ya bayyana wannan yunkuri a matsayin yiwa dimokradiyya karan tsaye.
Haka kuma ya bayyana cewa, jam’iyyar tasu ta PDP ta aikewa rundunar ‘Yan Sandan a rubuce cewa zata gudanar da wannan taro a wannan rana kuma a wannan lokaci kuma rundunar ta amince musu su yi taronsu.

“Amma abun kunya sai a yau da safiyar wannan rana ta taro bayan mun gayyato al’ummarmu samada mutun dubu 150 suna kan hanyar zuwa, sannan kwamishinan ‘Yan Sanda ya bugawa shugaban kwamitin tsaro na kamfen dinmu a jiha cewa lallai sai mu dage wannan taro daga wannan rana wai ranar kasuwa ce”,
“Bayan kuma kowa ya sani tunda aka kafa jam’iyyar PDP samada shekaru ashirin a wannan rana muke gudanar da taronmu kuma a bamu taba hana wani sakewa, sannan kuma su dakansu suka amince mana muyi taronmu a lokacin da muka aike musu” inji Gumel.
Haka kuma ya yi barazanar gurfanar da rundunar ‘Yan Sandan da gwamnatin jihar Jigawa gaban kuliya‎ domin a cewarsa sune suke da hannu wajen hanasu wannan taro.
“Ina so in tabbatar muku cewa, wannan yiwa dokar kasa karan tsaye duk da cewar‎ kuwa dokar ce ta samarda shugaban kasa, shugaban rundunar ta ‘Yan Sanda da kuma shi kansa kwamishinan don haka ba zamu yarda ba dole ne mu nemi hakkinmu” inji Gumel.

LEADERSHIP A Yau ta tuntubi kakakin rundunar ‘Yan Sanda reshen jihar ta Jigawa SP Abdul Jinjiri wadda ya ce zuwa yanzu ba’a sanarda shi komai kan wannan batu ba amma zarar an sanarda shi zai mana karin bayani.
Shi kuwa da yake maida martani kan wannan zargi, kwamishinan ‘yansanda reshen jihar Jigawa CP Bala Zama Senchi ya ce ko daya wannan batu ba haka yake ba, illa‎ kawai jam’iyyar ta PDP sun yi yunkurin yin kunnen shegu da doka.
Ya bayyana cewa, “kamar kowacce jam’iyya, sun ‎aiko mana da jadawalin tarurrukansu kuma sun sanya wannan rana a matsayin ranar da zasu gudanarda taronsu a yankin Hadeja ba Gumel ba, amma daga baya suka ce tunda ana alhinin rasuwar Hamza Abdullahi a Hadeja zasu sauya shi zuwa Gumel kuma muka amince”
“Daga bisani mun sami labarin wannan taro a G‎umel zasu gudanar da shi a Kasuwa wadda kuma a wannan rana take ci, don haka ni da kaina na kira shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Sule Lamido da kuma shugaban kwamitin tsaro na kamfen dinsu kan cewa su sauya wurin taron nan zuwa filin wasa na Gumel ko duk wani gurin da suke bukata amma banda kasuwa’ domin yin taron cikin kasuwa kan iya haifar da wata matsala a fannin tsaro, amma suka kekasa kasa suka ce a’a, wannan shi ne gaskiyar abin da ya faru” inji Kwamishinan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!