Connect with us

SIYASA

‘Yan Takarar Gwamna A Jihar Filato Sun Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya  

Published

on

‘Yan Takarar Gwamna a jihar Filato sun sanya hannu a wata takardar yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe da bayan zaben 2019 a fadin jihar.

Kamfanin dillancin labarai ta labarto cewa; yarjejeniyar wanda Gwamnan jihar Simon Lalong ya fara sanyawa hannun, sannan sai dan takarar gwamnan a jam’iyyar PDP Sanata Jeremiah Useni, sai sauran ‘yan takarar gwamna 12.

Cibiyar DREP ita ce ta shirya wannan taron.

Babban Bishaf Ignatius Kaigama, wanda yake shi ne ciyaman din wannan cibiya, ya bayyana cewa; manufar sanya hannu a waannan yarjejeniyar shi ne domin dakile aukuwar rigima.

Kaigama ya shawarci ‘yan takarar da su yi hankali da amfani da kalaman batanci, zage-zage da cin mutunci a yayin kamfen dinsu domin gudun haifar da rikici. Sannan ya bukaci da ‘yan takarar da su ja kunnen magoya bayansu da su zama masu son zaman lafiya. Babban Bishaf din ya ci gaba da cewa; yana da kyau masu fada a ji a jihar, sun nesanci tad a husuma da sunan siyasa. Sannan su kiyaye siyasar gaba da kiyayya.

Rahotanni sun nuna cewa akalla akwai ‘yan takara 21 da suke neman gwamna a jihar Filato a jam’iyyu daban-daban.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!