Connect with us

RA'AYINMU

A Kawo Karshen Ukubar Da ‘Yan Gudun Hijira Ke Sha

Published

on

Ko shakka babu ci gaba da zaman ‘yan gudun hijira a sansanoninsu musamman a yankunan Arewa maso gabas, gazawa ce ga gwamnatin Nijeriya. Wadannan ‘yan gudun hijira sun fara samun kansu a wannan tasku tun a shekarar 2009 sakamakon rikicin ‘yan ta’adda na Boko Haram, daga baya-baya kuma rikicin manoma da makiyaya, rikicin wasu daga cikin jihohin Arewa ta tsakiya da kuma yawaitar kashe-kashen al’umma babu ji babu gani a Jihohin Zamfara da makwaftanta.
Wannan rikice-rikice da bala’o’i da suka addabi al’ummar wadannan yankuna da sauran makamantan su, ya sa ake ganin Nijeriya na daya daga cikin kasar ta fi kowace kasa a duniya yawan ‘yan gudun hijira. Haka zalika, wani rahoto ya nuna cewa, kowane sansani na ‘yan gudun hijirar na dauke da cincirundon mutane da sakamakon hakan ke saurin haifar da cututtuka, rashin watayawa, zinace-zinace da karuwanci da sauran miyagun laifuka. A hannu guda kuma, wadanda ke da alhakin kula ko magance wadannan matsaloli sun buge da ihu a kan kawo karshen cutar kanjamau da cin hanci da rashawa.
A shekarar da ta gabata, kididdiga ta nuna cewa an samu kimanin ‘yan gudun hijira a jihohi shida na Arewa maso gabas dai-dai har Milyan daya da dubu dari bakwai a gidajen mutane daban-daban sama da gida 321,580, tare da cewa kaso arba’in na ‘yan gudun hijirar na zaune ne a sansanoninsu da ke cikin birane. Haka zalika idan aka hada da yawan adadin ‘yan gudun hijirar da rikicin yankunan Arewa ta tsakiya da kuma Arewa maso gabas ya rutsa da su, sun tasamma Milyan biyu. Ga duk mai hankali ya san warwatsuwar wadannan dandazon ‘yan gudun hijira tare da yawaitar kashe-kashe da rikice-rikice da ake ci gaba da samu a wadannan yankuna, ba karamar barazana ce ga gwamnatin Nijeriya ba.
Har ila yau, rahotanni da dama sun bayyana irin mawuyacin hali tare da kunci da wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar ke fuskanta a sansanonin nasu. Mafiya yawan su na fama da matsalar yunwa, rashin samun cikakkiyar kulawa ta fuskar lafiya, matsalar karancin dakunan kwana, yawaitar fyade da sauran makamantansu. Kananan yara su ne mafi ta’azzara a wadannan sansanoni don kuwa su suka fi saurin daukar cututtuka iri daban-daban da ke saurin halaka dan Adam, kamar cutar cizon sauro, amai da gudawa, tarin fuka, yunwa da sauran makamantan su.
Sau tari, mafiya yawan sansanonin ‘yan gudun hijirar sun dogara ne da gudunmawar da suke samu daga kauyukan da ke kewaye da su, daidaikun mutane masu ba da taimako da sauran kungiyoyi masu zaman kansu na gida da na waje fiye da tallafin da Hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA) da Hukumar da gwamnati ta dorawa alhakin kula da ‘yan gudun jirar. Babu shakka wannan dalili na kara sanya wadannan ‘yan gudun hijira cikin mawuyacin hali, maimakon a ce su ma a matsayinsu na ‘yan Nijeriya sun samu dama ko ‘yancin sake dawowa matsugunansu don ci gaba da rayuwa kamar sauran al’ummar wannan kasa.
Haka zalika, babu dalilin da zai sa a ce gwamnati ta sakarwa daidaikun masu ba da gudunmawa, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran kasashen ketare ragamar kulawa da wadannan ‘yan gudun hijira, don kuwa yin hakan zai ci gaba da sanya su cikin halin ni ‘ya su. A maimakon wannan gidan Jarida, muna sake kira ga gwamnatoci daga sama har kasa da a kula da halin da sansanonin ‘yan gudun hijira na cikin kasar nan baki daya ke ciki, musamman a bangaren abinci da kuma kula da lafiyarsu har zuwa lokacin da Allah zai kawo zaman lafiya a gurarensu kowa ya koma mahaifarsa. Haka nan, muna sake kira ga gwamnati da ta yi wani hobasa na ba su horo na musamman a bangaren sana’o’i da ilmi don samun abinda za su shagaltu da shi su kuma dogara da kawunansu.
A karshe, ya zama wajibi Hukomomin tsaro su sake kara kaimi wajen yaki da ta’addanci da kuma ‘yan ta’adda a fadin wadannan yankuna don bawa ‘yan gudun hijirar damar komawa matsugunansu. Don kuwa matsawar wadannan rikice-rikice na ci gaba da wanzuwa a wadannan yankuna, ‘yan gudun hijirar su ma za su ci gaba da zama a cikin hali kaka-na- ka-yi, wannan dalili ne ma ya sa har suka fara yin bore a ranar wata Litinin 24 ga Disamba, 2018, a karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara game da rashin jin dadinsu a kan yadda ake yi musu kisan gilla da kuma ita kanta gwamnati don kin daukar matakin da ya dace ga ‘yan ta’addan don samun dorarren zaman lafiya a yankunan nasu.
Babban burinmu shi ne ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, shi yasa muke sake kira ga gwamnati a kowane irin mataki ta tabbata ba ta bawa wadannan ‘yan gudun hijira damar nemawa kansu da kansu makoma ba, don kuwa yin hakan zai iya haifar da da maras ido. Jihohi da gwamnatin tarayya su tabbata sun baiwa ‘yan gudun hijira kulawa ta musamman, sannan su hukunta duk wani wanda ke ci da guminsu ko wani abu makamancin haka. Sannan a zo a hada hannu da hannaye wuri guda a kawar da ta’addanci da ‘yan ta’adda a kuma tabbata kowane dan gudun hijira a wannan kasa ya koma mahaifarsa an samu dorarren zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!