Connect with us

LABARAI

Ba A Daga Babban Maulidin Duniya Na Gobe A Kebbi Ba – Alkasim Yauri

Published

on

Babban Sakataren Jam’iyyatu Ansaruddeen Attijjaniya, Muhammad Alkasim Yahaya ya bayyana cewa Babban Maulin Shehu Ibrahim Inyas na Duniya da za a yi a Birnin Kebbi yana nan daram ba daga shi ba kamar yadda wasu ke rade-radi.
Alkasim Yauri, ya bayyana haka ne a yayin tattanawa da manema labarai a jiya Alhamis a Birnin Kebbi, yana mai cewa taron mauludin wanda shi ne irinsa na farko da aka taba yi a tarihin Tijjaniyya a kasar nan, zai samu halartar manyan malamai daga sassa na duniya daban-daban da suka hada da Murtaniya da Misra da Senigal da sauransu.
Ya ce “wannan taro ba a daga shi ba, yana nan wanda za a tattauna rayuwar Manzon Allah (SAW) da kuma ainihin soyayyar Manzon Allah, domin soyayyar Annabi ita ce gari a Musulunci, tana sama da komai. Kuma wannan taro zamu iya cewa wata babbar jami’a ce zamu bude na soyayyar manzon Allah, domin zamu kwanki biyu ne, daga Alhamis zuwa Asabar a Birnin Kebbi,” a cewarsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!