Connect with us

SIYASA

Dan Majalisa Zai Samar Da Rediyon FM Da Kamfanin Fenti A Jihar Kebbi

Published

on

Alhaji Shehu Muhammad, dan takarar majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar APC mai wakiltar Maiyama/Koko/Besse ya yi alkawarin samar da kamfanin yin fenti a matsayin wani mataki domin rage rashin aikin yi a jihar Kebbi.

Muhammad ya fadawa kamfanin dillancin labarai a yau Juma’a a Birnin Kebbi cewa; idan ya samar da wannan Kamfani na yin fenti da hada alli, sama da matasa 200 ne za su samu aikin yi. Ya ci gaba da cewa; sun hada yarjejeniya da kamfanin Julius Berger domin ganin ya samar da wannan kamfani. Ya ce; sun cimma wannan yarjejeniyar watanni 4 da suka gabata.

Ya tabbatar da cewa; manufar shi ne rage yawan marasa aikin yi, da kuma ba su damar nuna kwarewarsu da bajintarsu a bangaren kasuwanci, ya ce; idan har suka yi nasara, wata rana suma za su dauki wadansu ayyuka. Ya tabbatar da cewa; suna tsammanin za a cimma wannan kwangilar cikin shekarar 2019. Ya ce; a halin yanzu an biya kashi 25 na kwangilar.

Sannan ya kara da cewa; zai samar da gidan rediyo FM mai zaman kansa, wanda zai yi shi a mazabarsa domin ganin shima ya samarwa da wadansu matasan ayyukan yi, tare da bunkasa ‘yancin fadar albarkacin baki. Ya ce; burinsa shi ne ya samar da gidan Rediyo mai nisan kilomita 200. Ya kara da cewa; a halin yanzu ya samu lasisin yin hakan, kuma zai yi shi ne a yankin Koko.

A karshe ya shawarci matasa su guji ayyaukan dabanci da ta hargitsi a lokacin zabe da bayan zabe.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!