Connect with us

LABARAI

Gwamna Ganduje Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni Hudu

Published

on

Da yammacin ranar Laraba ne Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci Rantsar da sabbin Kwamishinoni hudu bayan kammala tantancewar da Majalisar Dokokin Jihar Kano da kuma bangarorin tsaro suka gudanar.
Kwamishinonin sun hada da Alhaji Mukhtar Ishak Yakasai wanda aka tura Ma’aikatar Ayyuka na Musamman, Hon. Shehu Kura Muhammad Na’allah wanda aka tura ma’aikatar kasafin kudi, Alhaji Bashir Yahaya Karaye wanda aka tura ma’aikatar Ilimin Kimiyya da fasaha, Malam Ibraim Baba impossible wanda aka tura Ma’aikata Ilimi mai zurfi.
Haka kuma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sauya wurin aikin tsohuwar Kwamishinan kasafin kudi Hajiya Aisha Jafa’ar wadda aka mayar da ita ma’aikatar ilimi ta Jihar Kano.
An gudanar da bikin rantsar da sabbin Kwamishinonin tare da kaddamar
da Kwamitin yakin neman zaben Gwamna Ganduje na shekara ta 2019 wanda aka gudanar a dakin taro na Coronation da ke fadar Gwamnatin Kano.
Taron ya samu halartar Gwamna Dakta Abdullahi Umar Gnaduje, Mataimakin Gwamna Dakta Nasiru Yusif Gawuna, Tsohon Gwamnan Kano Kuma dan takarar Kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano,
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas da sauran jami’an Gwamnati da ‘yan siyasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!