Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Jigawa Ta Karawa Malaman Makarantu 14,900 Girma A Shekarar 2018 –NUT

Published

on

Kungiyar Malaman Nijeriya wato NUT, reshen jihar Jigawa sun bayyana cewa; gwamnatin jihar Jigawa ta karawa Malaman makaranta dubu 14 da 900 karin girma a cikin shekarar 2018.

Shugaban kungiyar, Alhaji Abdulkadir Yunusa, shi ne ya bayyanawa manema labarai a yau Juma’a a garin Hadeija.

Ya ci gaba da cewa; Malaman Firamare da na karamar Sakandare dubu 12,000 ne suka samu karin girma. Yayin da Malaman Sakandare dubu 2 da dari 900 ne suka samu karin girman.

Yunusa ya ci gaba da cewa; har wala yau gwamnatin ta horas da sabbin Malaman Firamare 2,000 sai Malaman Sakandare 750 duk a cikin shekarar 2018.

Ya ci gaba da cewa; Malamai 514 suka yi rijista da hukumar shirya Jarabawar Malamai a cikin shekarar. A karshe, shugaban ya yi kira ga Malaman da su tabbata sun yi rijista da hukumar domin kaucewa hana su gudanar da ayyukansu.

Ya karkare da cewa; “Ko digiri kake da shi ko NCE, rashin yin rijista da hukumar, ba za mu lamunta ba.” Inji shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!