Connect with us

WASANNI

Hazard Ya Fi Karfin Zama A Chelsea – Jenas

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Jermaine Jenas, ya ce a halin yanzu kwarewa da kwazon dan wasan gaba na Chelsea Eden Hazard, ya fi karfin kungiyar tasa kuma yana bukatar babbar kungiya.
Jenas ya bayyana haka ne, yayin da yake tsokaci kan wasan kusa dana karshe na kofin Carabao da aka sani da Carlin a baya, wanda a ranar Talata Tottenham ta samu nasara kan Chelsea da 1-0 a filin wasa na Wembley dake birnin Landan.
Tsohon dan wasan na Tottenham, ya ce lokaci yayi da Hazard mai shekaru 28, zai rabu da Chelsea ya koma wata babbar kungiya a nahiyar ta Turai, saboda yadda kwarewar dan wasan ta girmi kungiyar tasa.
An dai jima ana alakanta Eden Hazard da rahotannin yana shirin sauya sheka daga Chelsea zuwa Real Madrid, zalika shi kansa dan wasan ya sha bayyana sha’awar komawa kungiyar ta Real Madrid, sai dai kawo yanzu hakan bai tabbata ba.
Yarjejeniyar Hazard da Chelsea za ta kare a shekarar 2020, kuma har yanzu bai sa hannu kan kara wa’adinta ba hakan yake nuna tabbas dan wasan wanda yakoma Chelsea daga Marseille yanason sauya sheka.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tayi kokarin siyan dan wasan domin ya maye mata gurbin dan wasa Crystiano Ronaldo wanda yabar kungiyar zuwa Jubentus sai dai Chelsea tayi kokarin hanshi tafiya
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!