Connect with us

LABARAI

Hukumar NITDA Ta Sha Alwashin  Sanya Masu Samar Da Intanet Bin Dokoki

Published

on

Hukumar ci gaban bayanai da fasaha ta kasa wato NITDA ta jaddada alkawarinta cewa; za ta tabbatar da cewa masu samar wa al’umma Intanet (PIA) sun bi dokokin hukumar.

Babban Darakta Janar na hukumar Dk. Isa Pantami, shi ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a birnin tarayya Abuja. Ya bayyana cewa; wannan mataki yana daga cikin matakan da hukumar na bunkasa bangaren bayanai da fasaha a Nijeriya.

Dokokin da suka shafi PIA, doka ce ta shafi samar da Intanet ga al’umma musamman inda al’umma ke da damar amfani da Intanet.

Pantami ya ce hukumarsa ta NITDA, bisa la’akari da dokokin bunkasa bangaren bayanai da fasaha a Nijeriya, sun shirya tsaf domin zartar da dokar da ta shafi PIA sashe na 6  na NITDA Act 2007.

Hukumar NITDA ta jinjinawa masu samar da Intanet din, domin a cewarsa suna cikin kasuwancin bunkasa bangaren bayanai da fasaha a kasarnan ta hanyar bunkasa hanyoyin amfani da Intanet.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!