Connect with us

MU KOYI ADDINI

Idan Na Yi Kaki Ina Ganin Gashi A Ciki, Ina Mafita?

Published

on

Assalamu Alaikum, Malam akwai wani abu da yake damuna wajan wata uku baya, wani lokaci in na yi kaki sai na dunga ganin gashi a cikin kakin, ko kuma in yana bakina sai na ji gashi ina fito da shi, shi ne Malam na kasa samun sukuni, dan Allah Malam meye kuma mai ya kamata na yi?
Wa’alaikum assalam, Ina baka shawarar ka rike azkar na safiya da yammaci, da kuma na shiga bandaki da na shiga gida da fita, da addu’o’in kwanciya bacci, saboda suna kariya daga fitintinu, sannan ka yawaita istigfari saboda zunubai suna jawo bala’o’i, ka kuma kula da hakkokin bayin Allah dake kanka, in har ba ka daina ganin gashin ba, kana iya zuwa wajan likita don ka ga ko akwai abin da zai iya yi.
Allah ne mafi Sani.

Fifita Tsakanin Kishiyoyi Haramun Ne!
Assalamu Alaikum. Malam na kasance inna kyautata ma mijina iya gwargwadona, to amma matsalar ba ni kadai ba ce sai yakasance ni ma yana mun duk wani abu na jin dadi da kyautatawa fiye da kishiyar tawa, wani lokacin ma ba ya boyewa, to shin malam ba ma Shiga hakkinta, kuma mene ne hukuncin haka? Na gode.
Wa’alaikum assalam Ya wajaba ayi adalci a lamura na zahiri (kamar abinci, tufa) tsakanin kishiyoyi, Annabi (SAW) yana cewa: “Duk Wanda yake da mata biyu, amma bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar alkiyama sahensa daya a shagide”.
Ya halatta in kana da mata guda biyu ka fi son daya daga ciki, ka fi jin dadin saduwa da ita, ka fi dadewa a dakinta, Annabi (SAW) ya fi son nana Aisha akan duka matansa tara da ya mutu ya bari, kuma matansa da sahabbansa sun san hakan, kamar yadda ya tabbata a sahihul Bukhari.
Allah ne mafi sani.

Dole Sai Na Cire Hakorin Makka Saboda Kauce Wa Lam’a A Alwalata?
Malam da gaske ne da ake cewa hakorin Makka lam’a ne? saboda ruwan alwala ba ya taba ainihin hakorin mutum?
To malam a zance mafi inganci, bai zama dole ruwan kurkure baki sai ya game dukkan hakora ba, saboda abin da ake nufi da kurkure baki shi ne zagaya ruwa a baki a fito da shi, don haka hakorin Makka ba zai kawo lam’a ba, amma kuma wasu malaman suna ganin kurkure baki ba zai cika ba sai ruwan ya game, don haka barin sanya hakorin Makka Shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai abin so ne.
Ya wajaba ga maza su guji sanya hakorin zinare, saboda Allah ya haramta zinare ga mazan al’umar Annabi Muhammad (SAW) kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a Sunan dinsa a hadisi mai lamba ta: 1720.
Don neman karin bayani duba Alminhaj sharhin Müslim na Nawawy 3/105.
Allah ne mafi Sani.

Wanda Yake Gida, Zai Iya Hada Salloli Saboda Ruwan Sama?
Assalamu alaikum. Allah karawa malam ilimi da fahimta. Shin dan Allah malam ko mutum zai iya hada sallah shi kadai idan ana ruwa bashi da ikon zuwa masallaci? Nagode malam.
To dan’uwa malamai sun yi sabani akan mas’alar zuwa maganganu guda biyu:
1. Ya halatta ga wanda yake a gida ya hada salloli saboda ruwan sama, tun da ruksa ce Allah ya bawa mutane, don haka ta shafi kowa da kowa, wannan ita ce maganar Hanabila kamar yadda mai INSAAF ya ambata: 2\340.
2. Bai halatta ga wanda bai je sallar jam’i ba ya hada salloli saboda ruwan sama, saboda an yi sauki ne ga wadanda za su je masallaci don kar su jika jikinsu da ruwa, wannan wahalar kuma babu ita ga wanda ya yi sallah a gida, don haka rahusar ba za ta same shi ba, sannan kuma shari’a ta yi nufin ta kiyaye sallar jam’i shi ya sa ta saukaka wajan hada salloli a ruwan sama,don kar mutane su watse sallar jam’i ta tozarta, wannan ita ce maganar Imamu shafi’i a littafinsa Al’umm 1\195.
A fahimtata maganar karshe ta fi inganci, don haka wanda yake gida ba zai hada salloli ba.
Allah ne mafi sani.

Bambanci Tsakanin Riba (Profit) Da Riba (Interest)

Assalamu alaikum. Malam Don Allah ina da tambaya? wai miye riba a musulunci? kuma idan mutum ya sayi abu Naira 5 ya halatta ya sai da a kan Naiar 8?

Wa’alaykumussalam, to malama riba ta kasu kashi biyu:
1. Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.
2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa ‘yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu.
Duka wadannan nau’oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka.
Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar naira 8, wannan ba’a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar da Allah ya halatta, saidai ana so mutum ya saukaka idan yana siyar da kaya, Annabi s.aw. yana cewa : “Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai siyar da kaya yake rangwame.
Allah ne mafi sani

Zan Iya Komawa Wajen Tsohon Mijina Idan Na Biyu Ya Sake Ni Kafin Mu Sadu?
Assalamu Alaikum Malamina. Fatan Alkhairi a gareka, da fatan ka wuni lafiya cikin koshin lafiya. Malam dan Allah ina da tambaya kamar haka: (Mutum ne ya saki matarsa har saki (3) a lokuta daban-daban, to, sai wani bawan Allah ya zo ya aure ta, bayan ya aureta sai wata matsala ta shiga tsakaninsu kuma ya sake ta amma kuma ko sau daya bai taba saduwa da ita ba, to, yanzu Malam ko wancan tsohon mijin nata zai iya mayar da ita, tun da gashi ta yi aure amma saduwa ce kawai ba’a yi da ita ba? Allah ya kara taimakon ka Malam.
Wa alaikum assalam, ina har ba su sadu ba, to bai halatta ta auri wani ba, saboda lokacin da matar Rifa’ata ta auri wani bayan mijinta ya sake ta, ta so ta rabu da mijinta na biyun, ta koma wajan na farkon, kafin su sadu, Annabi s.a.w. ya hanata, inda ya ce mata : “Dole sai kin dandana dadinsa, shi ma ya dandana dadinki”, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta:5372, wannan sai ya nuna cewa aya ta : 230 a Suratul Bakara, ba aure kawai take nufi ba, tana nufin aure hade da saduwa su ne suke halatta mace ga mijinta na farko, saboda aikin Annabi s.a.w. da maganarsa su ne suke fassara Alkur’ani.
Allah ne mafi sani

Fatawar Rabon Gado (193)
Assalamu Alaikum. Malam, tambaya ta akan rabon gado ne. Mutum ne ya mutu,ba Mata,ba yaya,ba iyaye sai kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa da Dan uwa wadda suke uba daya sai wadanda suke uwa daya. To mallam ya rabon gadonsa zai kasance? Hafizakallah.
Wa alaikum assalam , za’a raba gida (6), a bawa kakarsa kashi daya, ‘yan uwan da suka hada uwa kashi biyu, ragowar sai a bawa dan’uwansa li’abbi.
Allah ne mafi sani.

Wanda Aka Yiwa Kyauta Bai Amsa Ba, Har Ya Mutu, Shin Zai Shiga Rabon Magada?
Assalamu alaikum. Dan Allah Ga wata tambaya ta gaggawa. Wata baiwar Allah ta sayi kaya da niyyar baiwa ‘yar uwarta, amma kafin ta bata sai ‘yar uwar ta rasu. Shin wannan sayayya ta shiga cikin kayan gado? Na gode.
To dan’uwa ba zai shiga rabon magada ba, saboda kyauta ba ta tabbata sai an amsa, Wannan ya sa lokacin da sayyadina Abubakar ya yiwa ‘yarsa Aisha kyauta ba ta amsa ba, Har mutuwa ta zo masa ya soke kyautar, ya mayar da ita dukiyar magada. Kamar yadda Malik ya rawaito a Muwada’i a hadisi mai lamba ta: 717. Wannan ita ce maganar mafi yawancin malamai.
Don neman Karin bayani duba: Al’umm na Shafi’I 4\64, da Bada’iussana’i’i 6\8.
Allah ne mafi sani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!