Connect with us

WASANNI

Ina Son Victor Moses Ya Janye Ritayarsa, In Ji Kocin Nijeriya

Published

on

Mai horar da tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya, Gernot Rohr, ya ce zai yi farin cikin ganin dan wasansa Victor Moses ya janye matakinsa na yin ritaya daga bugawa kasarsa kwallo.
Yayin da yake tsokaci kan matakin na Moses, Rohr ya ce Najeriya tana maraba da dawowarsa domin ci gaba da wakiltarta, musamman ma, idan dan wasan yana samun damar bugawa kungiyarsa a nahiyar turai wasanni sosai.
A shekarar 2018, Victor Moses ya sanar da yin ritaya daga bugawa Najeriya kwallo, yana da shekaru 27, kwanaki kadan, bayan kammala gasar cin kofin duniya da Rasha ta karbi bakunci, wadda Najeriya ta gaza fita daga matakin rukuni zuwa zagaye na gaba.
A waccan lokacin Moses ya ce ya yanke shawarar ce saboda ya samu damar lura da iyalansa, zalika zai mayar da hankali wajen karfafa kwazon wasannin dayake bugawa kungiyarsa ta Chelsea.
Sai dai ba kamar lokacin kakar wasa ta 2016/2017 ba yayin a zamanin horarwar Antonio Conte, bayan da sabon mai horarwa Maurizio Sarri ya karbi ragamar kungiyar Chelsea, wasanni kalilan kawai Moses ya samu bugawa, lamarin da ya tilasta mishi soma neman kungiyar da zai koma.
Tuni dai aka bayyana cewa kungiyoyi irinsu Fulham da Crystal Palace a gasar firimiya suan zawarcinsa domin yakoma yaci gaba da samun damar buga wasa yayinda wata kungiya wadda ba’a bayyana sunanta ba a kasar China take zawarcinsa domin yakoma can.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!