Connect with us

LABARAI

JAMB Ta Gargadi Dalibai Masu Amfani Da Lambar Waya Iri Daya  

Published

on

Hukumar dake shirya jarabawar sharer fage na shiga jami’a wato JAMB ta gargadi daliban masu rijistar jarabawar shekarar 2019 su guji kirkirarwa kansu matsaloli da kansu. Hukumar ta bayyana hakan ne a yau Juma’a ta hannun jami’in hulda da kafafen watsa labarai, Dk. Fabian Benjamin a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a jihar Legas.

An dai fara Rijistan jarabawar ne a jiya Alhamis 10 ga watan Janairun a wurare 700 da hukumar ta tantance su rika rijistar jarabawar.

Benjamin ya tabbatar da cewa; duk dalibin da yake son zana jarabawarnan ya fara aika cikakken sunansa, amma sunan mahaifinsa ya zo a farko zuwa ga namban da hukumar ta samar. Suka ce; a yayin yin hakan, dalibin ya tabbata ba wanda ya yi amfani da wannan namban wajen aikawa hukumar da nufin yin rijista da hukumar.

Ya tabbatar da cewa; dalibai su guji amfani da namba guda daya wajen yin rijistar sunaye da yawa, domin hakan sam bai dace ba. Ya ce; ba haka aka tsara ba, hatta ko daliban ‘yan’uwan juna ne ba a amince da su yi amfani da suna guda ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!