Connect with us

LABARAI

Jami’an Tsaro Sun Sha Alwashin Tabbatar Da Tsaro A Lokacin Zaven 2019 A Taraba

Published

on

Yayin da zaven 2019 ke qaratowa, hukumar zave ta qasa, reshen jihar taraba ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki na tattaunawa don shawo kan dukkannin matsaloli da za su kawo tseko wurin gudanar da zaben 2019 a jihar.
Shugaban hukumar zaben Alhaji Baba Abba Yusuf, ya kira wannan taro na gaggawa a babban birnin jihar, Jalingo fadar jiha.
Taron ganawar ta qumshi jami’an tsaro na dukkannin rassa waxanda sun haxa da kwamishinan ‘yansanda da shugaban jami’an tsaro masu kare fararen hula (NSCD), da ma Babban jami’in tsaron farin kaya SSS da shugaban ‘yan bautar kasa ta jihar.
Sauran su ne, sarakunan gargajiya da shuwagabannin addinai, shuwagabannin dukkannin jam’iyu da matasa dama qungiyan mata dana ‘yan jaridu don ganin cewa kowannensu ya ba da tasa gudumowa wajen tabbatar da an gudanar da zabe mai inganci a watan faburairu da watan maris na 2019.
Yusuf ya ce duk wata nasara da za a cimma a harkar zaben da zai gudana, na daga cikin muhimmiyar rawa da masu ruwa da tsaki za su taka, wannan ne ma yasanya hukumar ta buqaci kowane bangare na jam’iyyu da hukumar tsaro da su haxa qarfi da qarfe wajen samar da mafita kan siyasar jihar ta Taraba.
Shugaban hukumar ta INEC, ya kara da cewa shawarwari daga ‘yan jaridu musamman ma ta yadda zabe zai gudana ba tare da wata katsalandan ba da irin gudummowa da ‘yan jaridu ke bayarwa wajen sanar wa al’umma na da matukar tasiri a wannan zabe. A in da ya ce hukumar na matukar godiya da jinjina ga ‘yan jaridun bisa fadakarwa da ilmantar da al’umma a baya can da ma a yanzun.
Sa’annan hukumar ta ce nan da kwana talatin da takwas za a fara zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun taraiya wadda da wannan ne ma ya sanya hukumar ta ce ranar biyu ga watan xaya na 2019, ta fitar da takardar shaidar zabe na kowace karamar hukuma da ke jihohi baki daya.

A nasa jawabin, kwamishinan ‘yansanda Mr. David Akinremi wanda ya yi jawabi a madadin jami’an tsaron jihar, ya yi nuni da cewa a shirye suke tsaf wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a dukkannin sassan jihar.

Akinremi ya gargadi al’umma da cewa ba za su bar wani ko wata kungiya ta rika kaiwa mutane hare-hare da karya doka ba. A cewarsa, wannan ne ma zai sanya su qara jajircewa wajen kare dukkannin xan kasa.

Daga cikin masu ruwa da tsaki da suka yi bayanai a gurin taron sun bukaci hukumar zaben da ta maida hankali kan mata, musamman masu juna biyu da iyaye mata dama masu yawan shekaru, kana sun bukaci jami’an tsaron da kada su sake ‘yan siyasa su yi amfani da su wajen juya zabe da mara ma wani xan takara baya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!