Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Kwana Nawa Courtois Zai Yi Ya Na Jinya?

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sanar da cewar mai tsaron ragarta Thibaut Courtois, zai yi jinyar kwanaki 10, yayinda bai buga wasan da kungiyar ta buga ban a gasar Copa del Rey da Leganes a ranar Laraba.
Haka kuma golan ba zai buga gasar La Liga da Real Madrid za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Real Betis da za su kece raini a filin wasa na Estadio Benito Billamarin ba kamar yadda kungiyar ta bayyana.
Ana sa ran Courtois zai murmmure kafin wasan La Liga da Real Madrid za ta yi da Sebilla a sati na sama wasan da kungiyar take fatan rama rashin nasarar da tayi a hannun Sebilla daci 3-0 a watan Oktoban daya gabata.
“Courtois yasamu rauni a hannunsa na dama hakan yasa zaiyi ‘yar gajeriyar jinya wadda bazata dauki tsawon lokaci ba kuma likitocinmu suna nan tare dashi suna kula da yanayin ciwon nasa” in ji Real Madrid a shafinta na yanar gizo
‘Kungiyar taci gaba da cewa muna yiwa Courtois fatan alheri da fatan kuma zai warware kafin sati mai zuwa sannan kuma muna sake jinjinawa magoya bayanmu bisa goyon bayan da suke bamu a koda yaushe”
Real Madrid dai tasamu nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Legannes a gasar cin kofin Copa Del Rey da suka buga a filin wasa na Santiago wasan da suka samu nasara daci 3-0 kuma a sati mai zuwa ne suma zasu kai ziyara gidan kungiyar ta Legannes
Sauran ‘yan kwallon Real Madrid da ke jinya sun hada da dan wasan gaba Gareth Bale dana tsakiya Toni Kroos da Jabi Sanchez da kuma dan wasan gaba Mariano wanda kungiyar ta siyo zai maye gurmin Ronaldo.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!