Connect with us

LABARAI

Labarin Kanzon Kurege Ya Taba Hada Ni Husuma Da Matata –Osinbajo

Published

on

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya koka kan irin illar da labaran kanzon kurege (karya) kan iya haddasarwa, inda ya bayyana yanda husuma ta shiga tsakaninsa da matarsa.
A lokacin da yake jawabi a wurin wani taro kan ‘Yaki Da Labaran Karya’ da BBC ta shirya a Abuja raanr Laraba, ya ce, wani marubuci a kafar sadarwa ta zamani ya dora wani hotonsa da wata mata da ta yi shigar banza tana bayyana tsiraicinta.
Osinbajo ya ce, bayan da ya yi dogon bincike da nazari a kan hoton, sai ya gano cewar, eh hak ane ya taba daukar hoto da matar, amma a lokacin ta yi shigar kirki ne. Ya kara da cewar, mai rubutun ya yi amfani da hoton matar ne inda take da shigar tsiraici sai ya hada da nashi.
“Ina cikin wadanda aka fi hari da labaran kanzon kurege. Wani lokaci zai iya jaza maka matsala da iyalinka. Kimanin sati biyu zuwa uku, na samu kira daga matata take tambaya ta cewa: Me ya hada ka da matan banza? Na ce mata kamar ya? ta ce ta karanta labari da yake cewa, ‘An kama Osinbajo Da Matan Banza’.
“Bayan bincike da dogon nazari a kan hoton da, sai na gane cewa, wadannan matan da aka nuna ni a tare dasu, na taba daukar hoto da su a yayin wani taro; amma lokacin suna da shiga ne kammalalla ba ta batsa ba, amma a wancan labarin da aka yada, sai aka canza hoton da wani; aka nuna kamar ina tare dasu ne a yayin da suke da waccan shigar.
“Daga baya na fahimci cewa, wancan hoton nasu da suka yi shigar tsitraici ba na lokacin da muka yi hoto tare bane, amma sai aka yi amfani da shi aka nuna cewa kamar ina tare dasu a lokacin da suke harkokinsu na holewa. Lalle matsalar labaran karya sun wuce yanda ake tunaninsu.”
Mataimakin Shugaban kasar ya ce, ba yau ne aka fara yada labaran karya ba; tsawon lokaci ana yi, amma akwai bukatar yaki da su saboda suna iya haddasa sabani ko rikici.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!