Connect with us

WASANNI

Levante Ta Lallasa Barcelona

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sha kaye a hannun kungiyar Levante a gasar kofin Copa del Rey ta kasar Sifaniya a jiya Alhamis.

Wannan ya biyo bayan rashin saka fitattun ‘yan wasanta guda biyu; Lionel Messi da Luis Suarez.

Erick Cabaco da Borja Mayoral, wadanda zaman wucin gadi ya kai su kungiyar Levante din daga kungiyar Real Madrid, sune suka fara zurawa Barcelona kwallo a ragarsu. Sai dai wasan an tashi ci 2 da 1 inda dan wasan Barcelona Coutinho ya yi nasarar zura kwallo guda a ragar Levante a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Wannan ya maishe da wasan aka tashi 2 da 1.

Wannan shi ne karo na farko da aka yi a jiyan, wanda masu sharhi akan kwallon kafa, suke ganin a karo na biyu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona suna iya yin nasara akan Levante din domin zuwa mataki na gaba a gasar, ganin yadda aka tashi wasan 2 da 1.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!