Connect with us

LABARAI

Mu Tsarkakakku Ne Yanzu, In Ji PDP

Published

on

Jam’iyyar PDP ta ce, Jam’iyyar ta yi waje da dukkanin shugabannin da ake zargi da sata daga cikin ta zuwa cikin Jam’iyyar APC.
Jam’iyyar ta PDP ta ce, yanzun kam mun tsarkakakku ne fes, sai dai ku nemi varayi a Jam’iyyar ta APC.
Jam’iyyar ta PDP ta faxi hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na harkokin siyasa, wanda Cocin, ‘Pentecostal Fellowship of Nigeria, da ke Ikeja, Lagos, ya shirya.
Jam’iyyu daban-daban ne da ‘yan takaran da suka fito daga mabambantan Jam’iyyua suka halarci taron, a lokacin taron, Jam’iyyun da kuma ‘yan takaran duk sun bayyana manufofin su da kuma shirye-shiryen su ga shugabannin Kiristocin da kuma sauran shugabannin al’umman da suka halarci taron.
Hakanan, wakilan hukumar zave mai zaman kanta ta qasa da wakilai daga hukumar wayar da kai ta qasa, duk suna daga cikin waxanda suka halarci taron.
Shugabannin Cocin na PFN, suka ce za su sanya ido sosai a kan yanda zaven zai gudana, za kuma su tura wakilansu biyar-biyar a kowace mazava da ke cikin garin Legas.
A lokacin da Jam’iyyun suke gabatar da manufofin na su ne, Jam’iyyar ta PDP ta ce ta mayar da dukkanin varayin shugabannin da a baya suke a cikin ta zuwa cikin Jam’iyyar APC.
“Mu ne kaxai Jam’iyyar da muka bi tsarin Dimokuraxiyya a wajen zavan shugabannin Jam’iyyarmu, har ma da xan takaran shugaban qasa na Jam’iyyar na mu.
“Duk Jam’iyyar da babu bin tsarin Dimokuraxiyya a cikinta, ba ta yanda za ta iya taimakawa Nijeriya fita daga cikin matsalolin da take a cikin su. Mu mun gwada hakan, kuma kowa ya gani.
“Kuma zargin satar duk da suke yi mana, a yanzun duk mun watsa masu varayin shugabannin Jam’iyyar zuwa cikin Jam’iyyarsu ta APC, kowa ya san hakan tabbas ne.
“Don haka a yanzun, PDP ta tsarkaka daga duk wani batun satar dukiyar qasa, a yanzun Jam’iyyar APC ce matattarar varayin qasa na shekaru 16 da suka shuxe,” in ji wanda ya wakilci Jam’iyyar ta PDP a wajen taron, Kunle Okunola.
Okunola, wanda xan takara ne a Majalisar Wakilai ta tarayya mai neman wakiltar mazavar Ikeja, a qarqashin Jam’iyyar ta PDP, ya ce Jam’iyyar ta PDP ce za ta sake fasalin zaman Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!