Connect with us

WASANNI

Muhammad Salah: CAF Ba Ta Yi Wa ‘Yan Wasan Cikin Gida Aldalci Ba – Edema

Published

on

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya, da ke buga bangaren tsakiya, Edema Fuludu, ya ce akwai gyara kan tsarin da hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Afrika CAF ke bi, wajen tantance gwarzon dan wasan nahiyar.
Fuludu, ya yi tsokaci kan hukumar ta CAF ce, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, kwana guda bayan da Muhammed Salah dan kasar Masar da ke kungiyar Liverpool a Ingila, ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na Afrika, a ranar Talata 8 ga watan Janairu 2019.
A cewar tsohon dan wasan na Najeriya, ya kamata hukumar CAF ta rika zabar gwarzon Afrika daga cikin wasannin da take shiryawa a Nahiyar kadai, ba tare da la’akari da wasannin Turai ba.
Edema Fuludu ya ce, ta hanyar bin shawararsa ce kawai, CAF za ta rika yi wa ‘yan wasan da ke buga gasannin nahiyar Afrika adalci, amma ba a koda yaushe a rika karrama ‘yan wasan da ke buga gasannin nahiyar Turai ba.
Edema Fuludu na cikin ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya, da suka lashe kofin gasar Afrika a shekarar 1994, da kasar Tunisia ta karbi bakunci kuma yaje gasar cin kofin duniya wanda aka buga a kasar Amurka.
Muhammad Salah dai ya doke abokan karawarsa wajen lashe kyautar da suka hada da takwaransa na Liverpool Sadio Mane dan kasar Senegal sai kuma Aubameyang na kungiyar Arsenal dan kasar Gabon.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!