Connect with us

SIYASA

Neman Tazarcen Buhari: Tasirin Tinubu Da Amaechi A Kan Sikeli

Published

on

A halin yanzu, za a iya cewa tukunyar siyasar zaben 2019 ta fara tausa bisa matakan da jam’iyyun siyasar da za su fafata a zaben ke ci gaba da dauka domin samun nasara.


A farkon makon nan, Jam’iyyar APC mai mulki ta kaddamar da tawagar dakarun da za su kasance a gaba wajen yi ma ta gwagwarmayar tsira da kambinta na kawo sauyi a kasar nan. Sai dai kuma, bisa irin tubalin da ta aza a tawagar, ‘Yan Nijeriya da dama masu bibiyar fagen siyasa sun shiga kogin tafakkurin gano musabbabin sanya manyan kwamandojin yakin neman zaben da dan takarar jam’iyyar na shugaban kasa kuma shugaba mai ci, Muhammadu Buhari ya yi.
Tun daga lokacin da Shugaba Buhari, ya shelanta shawarar da ya zartas na sanya tsohon Gwamnan Jihar Legas, Cif Bola Ahmed Tinubu, a matsayin cikakken jagoran jan ragamar yakin neman sake zabensa a lokacin kaddamar da tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na Jam’iyyar APC, wanda aka yi a Abuja, ranar Litinin, masu fashin bakin siyasa suke ta tofa albarkacin bakin su.
Wasu sun tafi ne a kan cewa, kila shugaba Buhari, ya dauki shawarar hakan ne domin ya nuna rashin tabbacin da yake da shi a kan babban daraktan kamfen din sake zaben na shi, Mista Rotimi Amaechi, a kan faifen maganan da ya bulla a kwanan nan, inda ake zargin cewa, Ministan na Sufuri ya ce, Shugaba Buhari, ba ya saurare kuma ba ya daukan shawara ba kuma ya yin nazarin samun bayanan halin da ake ciki. Wasu kuma suna da ra’ayin, shugaban kasan ya zartas da wannan shawarar ne a bisa yanda yake ganin mahimmancin jagoran Jam’iyyar sama da na tsohon Gwamnan na Jihar Ribas, a wajen neman sake zaben na shi.
Akwai kuma masu cewa, duk hakan wata dubara ce ta Shugaba Buhari na ganin ya janyo Tinubu din a jika sosai a kan harkar neman sake zaben na shi, a bisa masaniyar da yake da ita na raguwar shaharar sa matuka a wajen ‘yan Nijeriya, a kan hakan yake neman ya hada da karfin fada a jin da Bola Tinubun yake da shi a siyasance domin dai ya kai ga nasarar a sake zaben na shi, kamar kuma yanda wasu suke fadin, ai wata dubara ce kadai ta Shugaba Buhari, domin ya kaucewa fafatawan muhawarar ‘yan takaran shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 19 ga watan Janairu.
Buhari ya sha tsayawa takaran shugabancin kasa tun daga 2003 zuwa 2011, amma bai cin nasara, har sai da ya hada hannu da Jam’iyyar da Tinubu ke jagoranta ta CAN, inda suka kafa Jam’iyyar APC a shekarar 2015, sannan ne suka iya lashe zaben. Amma ba da jimawa ba da Buhari ya dare kujerar Shugabancin kasa, (kamar dai yanda ta saba faruwa a tsakanin ubannin gida na siyasa da wadanda suke dorawa a kasar nan) sai aka yi zargin Buhari din ya juyawa jagoran tafiyar (Tinubu) baya, har na kusan shekaru uku, har sai lokacin da ya fahimci irin mahimmancin da jagoran jam’iyyar yake da shi a wajen sake zaban na shi matukar dai da gaske yana neman samun nasara.
Alaka a tsakanin Buhari da Tinubu ta lalace matuka, inda har ta kai ga Uwargidan Buhari din Aisha, da Uwargidan Tinubu, Remi, sun koka a wasu lokutan. A sa’ilin da ita Aisha, take zargin wasu ‘yan ma’abba sun kankane a fadar shugaban kasa, sun kore ainihin wadanda suka bayar da gagarumar gudummawa, aka sha wahalar neman kujerar har kuma aka kai ga nasara tare da su a 2015. An ce Remi ta koka a kan yanda aka yi watsi da irin gudummawar da mijin nata ya bayar ga sabuwar jam’iyyar ta APC har ta kai ga nasara, tana mai cewa, an yi watsi da Maigidan nata.’
A hakanan sabanin da ke tsakanin Buhari da Tinubu ya ci gaba da karuwa a kullum, wanda hakan ya tilasta wa jagoran jam’iyyar (Tinubu) ya yi gudun hijira na kashin kansa har sai da lamuran kuma suka canza a kan yanda yake so a kwanan nan. Hakan ya faru ne a lokacin da Shugaba Buhari, ya fahimci irin matukar mahimmancin rawar da tsohon gwamnan na jihar Legas ya taka a siyasance, wanda har ya kai ga nasarar da aka samu a 2015.
Sai dai kuma, wasu masu fashin bakin suna ganin, Shugaban kasan dai yana sa ran Tinubu din ya sake maimaita siddabarun nasarar da ya yi amfani da ita ne a watan Satumba 2018, a kan zaben Gwamnan da aka yi a Jihar Osun, inda kiris ya rage ga Jam’iyyar hamayya ta PDP ta samu nasara, har sai da Tinubu din ya yi amfani da siddabarun na shi a zaben ‘yar kure ne lamarin ya canza APC ta sami nasara.
A lokacin da Tinubu ke ta faman takun-saka a tsakaninsa da fadar ta shugaban kasa, Amaechi da sauran ‘yan ma’abban da ake zargin sun mamaye fadar, suna can suna ta dasawa da gwangwajewar su a fadar, har ma ana zargin suna bin duk hanyar da suka sani ta ganin sun kaskantar da Jagoran na APC (Tinubu) tare da kisisinar tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Cif John Odigie-Oyegun. Akwai kuma masu hange da rade-radin cewa, Buhari ya yanke wannan shawarar ce a bisa ganin ba zai iya danka wannan mahimmin aikin na neman magoya baya da abokanan tafiya a kan Amaechi din ba, wanda yake tamkar Kwamanda ne wanda babu Sojoji a tare da shi.’


Tun a shekarar 2015 ne, ‘Janar’ Amaechi ya rasa kimar karfin siyasar da yake da shi, a inda ya gaza dora wanda yake so a kan kujerar Gwamnan Jihar na su ta Ribas a matsayin magajin sa a Jam’iyyar na su ta APC. Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ta hanyar amfani da karfin mulki irin na shugaban kasa, da kuma shaharar ikon da Uwargidansa, Dame Patience Jonathan, take da shi a Jihar, gami da irin karfin ginin siyasar da Nyesom Wike, ya kafa ne suka yi waje da duk wani karfin da Amaechin yake da shi a zaben Gwamanan da jini ya kwarara a Jihar a 2015.
Wasu masu sukan kuma, sun mayar da hankalin su a kan irin rawar siyasar da Amaechi din ya taka a Jihar, inda suka fitar da sakamakon cewa, bai samar ma da kansa shahara ta siyasa ba a Jihar na shi, ballantana ma a shiyyar na su ta Kudu maso kudu na kasar nan, hawa kujerar gwamnan Jihar ma da ya yi, wata kaddara ce kadai ta Allah. Tsohon gwamnan Jihar ta Ribas, Peter Odili, wanda Amaechi din ya yi aiki a matsayin mataimakinsa na kashin kansa a Fatakwal, an ce shi ne ya gyara masa hanyar shiga siyasar Jihar, inda ya bayar da shawarar a nada shi a matsayin mai taimakawa na musamman ga Gwamna Rufus Ada Geoge, a zamanin rusasshiyar jamhuriya ta uku.
Aka ce, ya sake samun bin ta wannan hanyar ne wajen samun nasara a kotu, wanda hakan ya kai shi zama dan majalisar jihar ta Ribas, inda a nan ne kuma ya sami nasarar zama Kakakin Majalisar jihar ta Ribas. Hakan kuma ya ba shi garabasar daukakar zama shugaban kungiyar shugabannin majalisun Jihohin Nijeriya, bayan na lokacin Dakta Olorunimbe Mamora, da hakan kuma ya tabbata a matsayin dan takara kwara daya tilo na kujerar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2006, wanda kuma da hakan ya dare kujerar gwamnan Jihar ta Ribas, a bisa hukuncin da kotun koli ta zartas.
Wike, wanda a wannan lokacin yake a matsayin shugaban karamar hukuma, shi ne ya tallafa masa wajen sake zaban sa a karo na biyu a shekarar 2003, a bisa yabawa da irin gudummawar da Amaechi din ya bayar, aka ce, “ya sadaukar da rayuwarsa a kan hadurra daban-daban, har dai ya kai ga yin gudun hijirar da Amaechi din ya yi, shi kuma ya jagoranci yakin na jiga-jigai a Jihar, wanda hakan ne ya baiwa Amaechi daman sake samun nasarar zama gwamnan Jihar ta Ribas a karo na biyu a shekarar 2007, bayan da aka yi ta sabarta-juyatta a kotuna, a karon na biyu.”
Da hakan ne, wasu masu nazarin ke cewa, sau guda ne kadai Amaechi ya ci wani zabe, gudan kuwa, Wike ne ya ciwo masa, a matsayin sa na babban daraktan yakin neman zaben gwamnan na shi. Aikin sa na farko a lokacin a matsayin sa na babban daraktan kamfen na shugaba Buhari, shi ne samun taimakon da ya yi ta hanyar nazartan dubarun da Wike ya bi a lokacin da ya yi masa kamfen.
Hakanan, zaben 2015 wanda ya yi sanadiyyar zama shugaban kasa da Buhari ya yi, ya sami dimbin kuri’u ne daga shiyyar arewaci da kuma kudu maso yammacin kasar nan ne, domin yawancin kuri’un kudu maso gabas da kudu maso kudu na kasar nan duk tsohon shugaban kasa Jonathan ne ya kwashe su, wanda hakan ke kara tabbatar da rashin karfin tsarin siyasar na Amaechi, a yankin na shi.
Duk a bisa hakan ne, ya sanya shugaba Buhari ya ga cewa kamata ya yi ya mayar da karfin kamfen din na shi ga Bola Tinubu, wanda ake ganin har yanzun yana nan da karfin sa na fada a ji a siyasar shiyyar ta Kudu maso yamma, yana kuma da karfi na kudi da zai iya karawa da duk wani mai ‘yan sulalla, ya kuma kawo sakamako mai kyau, in an kwatanta shi da Amaechi, wanda yake a matsayin daraktan kamfen din.
Sai dai, yana da kyau a lura, mika ragamar jagorancin kamfen din da Buhari ya yi ga Bola Tinubu, ba shi ne karo na farko da Shugaba Buharin yake neman kara kusanto da jagoran na Jam’iyyar APC kusa da shi ba. Ya dauki irin wadannan matakan sau da dama, wadanda suke nuna a shirye yake da ya aikata komai domin ya dadadawa tsohon Gwamnan na Jihar Legas da kuma shiyyar na shi ta kudu maso yamma kafin babban zaben na watan Fabrairu. Daya daga cikin irin wadannan matakan shi ne, nadin da shugaban kasan ya yi wa Tinubu na ya shugabanci kwamitin sasantawa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ta APC wadanda ba sa ga maciji da junansu, wanda wannan kwamitin bai iya cimma wata babbar nasara ba kafin a gabatar da babban taron jam’iyyar a watan Mayu na shekarar bara.
Hakanan, da gangan Buhari ya runsunawa Tinubu da jama’an sa a inda suka dage kan cewa, tilas ne tsohon shugaban jam’iyyar, Odigie-Oyegun, ya sauka daga shugabancin jam’iyyar a lokacin da aka yi babban taron jam’iyyar, duk da cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar sun bayar da shawarar a tsawaita lokacin shugabancin kwamitin gudanarwan jam’iyyar da Odigie-Oyegun ke wa shugabanci. Da farko shugaban kasan ya aminta da shawarar tsawaita lokacin na su, amma kwatsam daga baya sai ya canza shawarar hakan, ya runsunawa bukatar ta su Tinubu.
Hakanan, babu kuskure a kan cewa, kasantuwar shugaban jam’iyyar a halin yanzun, Adams Oshiomhole, a matsayin shugaban jam’iyyar, shi ma shawara ce ta jagoran jam’iyyar (Tinubu) wacce ta taras da amincewar shugaban kasan. Don haka, ba zai zama abin ta’ajibi ba, don Buhari ya danka wa Tinubu wuka da nama na kwamitin sake neman zaben na shi, a bisa dogaro da karfin siyasar na Tinubu a shiyyar kudu maso yamma na kasar nan, wanda ke da matukar mahimmanci ga Buhari na aniyarsa ta sake zama shugaban kasan.
A lokacin da yake shelanta sanarwar hakan, Buhari ya yi alkawarin aikinsa na gwamnati a matsayinsa na shugaban kasa, ba zai nakasa ba, a nan da kwanaki 40 duk da dawainiyar da ke kansa a nan gaba.
Buhari ya yi masaniya da wahalar da ke cikin kamfen din, sai ya bukaci Tinubu da mataimakin na shi a kan aikin kamfen din, da su dauki ragamar komai na yakin neman zaben kacokam. Buhari ya ce, “Duk da cewa, duk a tare ne za mu yi aikin kamfen din, amma ina tabbatarwa da kasa zan yi aikin da ya hau kaina ne ba tare da yin nakasa a harkokin tafiyar da kasar nan ba. Abokin shugabanci na, a wannan tawagar kamfen din, Tinubu, zai kasance shi ne cikakken jagoran kamfen din, shi ne mai sa ido a kan komai.”
To sai dai, me ke iya tabbatar da cewa, Buharin ba zai sake yin watsi da Tinubu din ba, a bayan ya sake darewa shugabancin kasa a karo na biyu, ya ma wulakanta Tinubu din fiye da yanda ya yi ma shi a karo na farko, tun da dai komai dai ya faru, Buharin ba abin da ya rasa daga Tinubu din. Sannan kuma akwai shaidun da ke tabbatar da shugaban kasan, kamar yanda wasu suke fadi na cewa bai iya cika alkawurran da ya dauka ba a lokacin yakin neman zabensa na 2015. Abin bakin cikin shi ne, Tinubu dai ba zai iya yin tutsu ba ga Shugaban kasan, saboda ya zama masa tilas ya yi biyayya, domin dalilan da suka sanya shi yin gudun hijira a baya suna nan, za kuma a iya sake nuna ma shi su ko gobe.
Sai dai, ana zargin Shugaban kasan da daukan wannan shawarar ne domin neman samun dimbin kuri’u daga shiyyar ta Kudu maso yamma. Kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta ce yin hakan yaudara ce kadai. Kakakin kungiyar, Mista Yinka Odumakin, ya ce duk wani yunkuri da shugaba Buhari zai yi na kaucewa kwamawar muhawarar ‘yan takaran shugabancin kasa da aka shirya gudanarwa a mako mai zuwa, zai iya haifar da mummunan sakamako a yunkurin da yake yi na ganin an sake zaben na shi. Yinka Odumakin ya ce, wannan nadin da ya yi wa Tinubu din akwai alamun yaudara a cikin sa, ya yi nuni da cewa, “An yi duk hakan ne domin ganin an dadadawa Tinubu, ya ji cewa, ana sane da mahimmancinsa. Amma dai koma mene ne, ana cewa, duk wanda bai dauki darasi daga abin da ya gabata ba, tabbas tarihi zai kara maimaita kansa.
A wani bangaren kuma, Shugaban jam’iyyar ADC, Cif Ralph Nwosu cewa ya yi, wannan shawarar gurguwa ce, ba kuma za ta haifar da wani sakamako mai kyau ba. Ya dage a kan cewa ai matukar dai Buhari ne wanda Jam’iyyar APC za ta tsayar. Ya yi nuni da cewa, ziyarar da ya kai sassan kasar nan daban-daban, ta tabbatar masa da al’umman kasar nan fa sun gaji da wannan gwamnatin ta Buhari, suna kuma neman canji ne.
“Jam’iyyar APC da Buhari, yaudarar siyasa ce kawai suke son yi,” in ji Nwosu. Za mu so sanin, wannan zaben za a gudanar da shi ne a tsakanin shugabancin Buhari, shugabancin Tinubu, ko shugabancin Jihar Legas? Masu kada kuri’a na kasar nan fa kansu ya waye, sun kuma fahimci cewa akwai fa gibi a fadar shugaban kasa. Masu kada kuri’a na kasar nan sun sha bakar yunwa da fama da rashin aikin yi a shekaru uku da suka shige. Hakan ya sanya suka sha alwashin kawar da wannan gwamnatin.
“A ziyarar da na kai a duk sassan kasar nan a wata guda da ya shige, ko’ina naje mutane cewa suke, suna son samun canji a fadar shugaban kasa, sukan kuma karanta mani irin gazawar da wanna gwamnatin ta yi. Duk mutane daga ma Kano da Daura, cewa suke yi suna son shugaban kasan da yake da kumarin yin aiki ne a fadar ta shugaban kasa.”
Sai dai kuma, wani dan Jam’iyyar ta APC, Mista Fouad Oki, cewa ya yi, shi bai ga wani rikitaccen abu ba a kan abin da shugaba Buhari din ya yi, tun da dai ya yi bayanin cewa, baya son kai-komon yakin neman zaben na shi ya yi wa aikin shugabancin da yake yi wa kasa tarnaki. Oki, ya yi watsi da jita-jitar cewa, Shugaba Buharin ya zabo Tinubu ne domin su yi shugabancin kamfen din a tare kasantuwar rashin lafiyar da yake fama da ita, da kuma neman hanyar kaucewa kai-komon yakin neman zaben a duk sassan kasar nan.
A cewar Oki, “In har ka fahimci yanda tsarin kwamitin na yakin neman zaben yake, daman tilas ne a sami shugaba da kuma mataimakin shugaba. A mafiya yawan lokuta, shi dan takaran, yakan kasance shi ne shugaba, sa’ilin kuma ga misali, a Jihar Legas, a inda na yi aiki sau da yawa a matsayin babban daraktan kamfen, mataimakin shugaban Jam’iyya a wasu lokutan a kan nada shi ne a matsayin shugaban kwamitin kamfen. Amma shi babban daraktan kamfen, tamkar daraktan gudanarwa ne kadai.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!