Connect with us

LABARAI

NNPC Za Ta Rage Farashin Iskar Gas

Published

on

Hukumar Man Fetur ta kasa wato NNPC ta ce tana wani shiri domin ganin ta rage farashin Iskar Gas a fadin kasarnan.

Ta ce; zata kaddamar da wannan ne ta hanyar kaddamar da tsarin kasuwanci nagartacce wanda zai kawo cikas da fitar sinadarin propane da butane daga kasarnan.

Babban Manajan Hukumar, sashen kasuwancin danyen man, Mallam Mele Kyari shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a jiya Alhamis A Abuja.

Ya ce sinadaran Propane da butane suna kan gaba wajen samar da iskar Gas din wanda ake yin girke-girke da shi.

Ya ci gaba da cewa; akwai shirin da suke yi wajen ganin an daina fitar da wadannan sinadaran na propane da butane daga kasarnan, wanda ya ce sashen kasuwancin danyen man na hukumar ne ke lura da shi, inda ya ce; za su tabbatar da an yi hakan domin bunkasa samar da iskar Gas din comin siyarwa a kasuwanncin gida. Ya ce; idan har aka yi hakan, farashin na Gas din zai ragu ya sauko a fadin kasarnan.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!