Connect with us

WASANNI

Pabard Ya Koma Bayern Munchen

Published

on

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Faransa, Benjamin Pabard zai koma kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da buga wasa ranar daya ga watan Yulin shekare ta 2019, kamar yadda kungiyar ta sanar.
Dan wasan wanda ya lashe kofin duniya a kasar Rasha, zai koma Bayern Munich da buga wasa daga kungiyar kwallon kafa ta Stuttgart dake kasar Jamus kan yarjejeniyar shekara biyar kan Yuro miliyan 35.
Pabard mai tsaron baya mai shekara 22 a duniya ya koma Stuttgard ne da buga kwallo daga kungiyar kwallon kafa ta Lille dake buga gasar rukuni rukuni ta kasar Faransa akan Yuro miliyan 11.
Dan wasan ya ci wa Faransa kwallo a karawar da ta yi nasara a kan kasar Argentina da ci 4-3 a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, wanda Faransa ta lashe kofin kuma babu wasan da dan wasan bai buga ba.
“Abin farin cikine samun damar buga wasa a kungiya kamar Munich saboda babbar kungiya ce wadda take da tarihi kuma ta lashe manyan kofuna a duniya sannan kuma tanada manyan ‘yan wasa’ in ji Pabard.
Yaci gaba da cewa “Akwai ‘yan wasa ‘yan asalin kasar Faransa da suka buga wasanni a kungiyar kuma sun bayar da gudunmawa sosai hakanne yasa nima nake ganin zan iya bayar da gudunmawa ta a Munich”
Karo na biyu Faransa na cin kofin duniya, bayan wanda ta fara dauka a gasar ta da karbi bakunci a shekara ta 1998 sai dai a shekara ta 2006 ta samu damar zuwa wasan karshe inda tayi rashin nasara a hannun kasar Italiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!