Connect with us

LABARAI

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Cafke Dan Boko Haram Da Ake Nema Ruwa A Jallo

Published

on

Rundunar Sojojin Nijeriya, sun cafke daya daga cikin membobin kungiyar Boko Haram wanda rundunar ke nema ruwa a jallo. Babagana Abubakar wanda aka fi sani da Alagarno shi ne wanda rundunar ta cafle. An kama shi ne a Bulabulim Ngarnam dake garin Maiduguri.

Mai magana da yawun rundunar Sojin, Birgediya Janaral Sani Usman, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a. Inda sanarwar ta kara da cewa; an kama Abubakar ne a lokacin da ya buya a wani daki dake wani gida a yankin Bulabulim Ngarnam.

Usman, ya ce; an samu hulanan kwano, Katin dan kasa da katunan zabe, rigar wasanni, kayayyakin Sojoji da sauran su a maboyar dan ta’addan. Ya ce; tuni aka yi awon gaba da shi, domin gudanar da bincike. Ya tabbatar da cewa; rundunar Sojin ta 195, ‘yan Sandan kwantar da tarzoma, da kuma ‘yan kato da gora na CJTF sune suka kama shi a jiya Alhamis.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!