Connect with us

LABARAI

Sabbin ‘Yan Gudun Hijira Sama Da 30,000 Suka Kwarara Zuwa Maiduguri – Majalisar Dinkin Duniya

Published

on

Hukumar kula da ayyukan jinkai ta majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewa ta dalilin tabarbarewar tsaron Boko Haram wanda ya yi kamari a ‘yan kwanakin nan, a yankin arewa maso-gabas ya jawo jama’ar wasu garuruwa kwarara a matsayin ‘yan gudun hijura sama da 30,000 zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wannan furucin ya fito ne daga bakin shuganan cibiyar ayyukan jinkan, a karkashin majalisar dinkin duniya a Nijeriya, Mista Edward Kallon, jiya Alhamis a Maiduguri.
Haka zalika kuma, ya bayyana damuwar su dangane da kwararar sabbin yan gudun hijirar, a baya bayan nan, ta dalilin kamarin hare-haren da ke ci gaba da zafafa a yankin.
“Wanda zancen da ake ciki yanzu, sama da ‘yan gudun hijura 30,000 suka isa birnin Maiduguri, wadanda akasarin su sun fito ne daga garin Baga, a makonnin da suka shige”.
“Kuma mafi yawan wadannan mutanen, sun shigo tun ranar 20 ga watan Disambar 2018, bayan dogon tafiya da suka yi a kafa, tare da kananan yara da tsoffi”.
“Wannan adadin, idan an hada da wani karin adadi na ‘yan hijira kimanin 20,000 wadanda suka yi matsugunni a ‘Teachers Billage’ da ke Maiduguri, wannan wajen ya yiwa musu karanci, ai nun”. Inji shi.
“Haka kuma bai kamata mutane su yi sansani a garin Monguno ba, saboda yadda ake da matukar bukatar tallafin jinkai; kamar irin su wurin kwana, abinci, ruwan sha da tsaftace muhalli”. Ya bayyana.
Mista Kallon ya yi wannan karin hasken a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a garin Monguno da sansanin gudun hijira a Teachers billage da ke Maiduguri.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!