Connect with us

LABARAI

Shugaban Kasa Buhari Ya Yi Alhinin Mutuwar Sarkin Sarakunan Jihar Nasarawa

Published

on

‑Saraki Ma Ya Mika Ta’aziyyarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa bisa labarin rasuwar Sarkin Sarakunan Nasarawa kuma mai Sarautar Lafiya, Alhaji Isah Mustapha Agwai I. Shugaban kasar ya aika da alhininsa ne ta hannun Malam Garba Shehu, mataimaki na musamman na shugaban kasar kan kafafen watsa labarai da hulda da jama’a. Inda ya mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar, Gwamna Umaru Tanko Al-Makura bisa rasuwar wannan Sarki.

Sannan ya mika ta’aziyyarsa ga Masarautar Lafiya, al’ummar Lafiya da Jihar Nasarawa baki daya. Shugaban kasar ya bayyana Agwai a matsayin wanda ya kare mutuncin masarautar. Ya ce; za a rika tuna Sarkin a matsayin wani gwarzo kuma abin koyi wanda ya yi aiki tukuru wajen bunkasa walwalar al’umma.

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dk. Bukola Saraki ya nuna alhininsa bisa rasuwar Sarkin Sarakunan jihar Nasarawa, Alhaji Isa Mustapha Agwai I. Inda shugaban Majalisar ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin.

Wannan sanarwa ta fito ne ta hannun mashawarci na musamman kan kafafen watsa labarai da hulda da jama’a na shugaban majalisar, Yusuph Olaniyonu, inda ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai son ci gaban kasa.

Saraki ya ce; Agwai mutum ne da ya yi aiki tukuru wa al’ummarsa, har ya zama Hakimin Obi, inda daga bisani aka nada shi a matsayin Sarkin Lafiya. Ya kara da cewa; Agwai mutum ne mai son zaman lafiya, ya ce; tabbas an yi babban rashi.

A karshe ya mika ta’aziyyarsa ga Iyalai, Masarautar Lafiya,

Alhaji Isa Mustapha Agwai I, Sarkin Lafiya, kuma Sarkin Sarakunan jihar Nasarawa, ya rasu ne a jiya Alhamis a wani asibiti a birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 84, ya bar mta 3 da ‘ya’ya 2.

An nada shi a matsayin Sarkin ne a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 1974, inda a kwanakin baya ya yi bikin murnar shekaru 44 da nada shi wannan mukamin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!