Connect with us

LABARAI

Wata Kungiya Ta Nemi Buhari Ya Kara Ma Sufeto Janar Na ‘Yan Sandan Wa’adi

Published

on

Ambasada Mukhtar Gashash, wanda yake shi ne shugaban kungiyarnan ta ‘Eminent Persons’ Forum’ reshen jihar Kano sun yi kira da babbar murya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara wa’adin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya, wato Ibrahim Idris.

Sun yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da suka kira wanda ya jagoranci kungiyoyin da ba na gwamnati ba, kungiyoyin kare hakkin al’umma, da sauran su a jihar Kano a Jiya Alhamis.

Mukhtar Gashash ya ce; wannan kira ya zama wajibi ne saboda irin nasarorin da shugaban ‘yan Sandan ke kawo wa kasarnan a bangaren tsaro ta hanyar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasarnan. Suka ce; da wannan suke kira ga shugaban kasar da kuma ‘yan majalisar kasar da a kara wa’adin Sufeto Janar na ‘yan Sandan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!