Connect with us

RA'AYI

Yadda Jamhuriyar Nijar Ke Wa Gwamnatin Buhari Da Nijeriya Zagon Kasa

Published

on

Idan har wani ko wasu na tababar yadda zaben shugaban kasa mai zuwa ke daukar hankali fiye da duk sauran zabukan da su ka gabata, to ya daina tababa ko waswasi, ya tsaya tsaf ya karanta wannan makalar.
Sai dai kuma kafin na fara cewa komai, bari na fara da yin matashiyar cewa ni dai ba dan siyasa ba ne; ni mai sharhi ne kawai a kan al’amurran yau da kullum. A bisa dalilin cewa duk abin da na ke yin sharhi a kai, ya shafe ni kuma ya shafi kasa ta Nijeriya da al’ummar cikin ta baki daya.
Wannan rubutu har ila yau, wata bulaliyar farkawa ce daga barci a kan dukkan ‘yan Nijeriya domin su tashi su gane wa idanun su misalai da dama na yadda gwamnatin Mahamadou Issofou ta Jamhuriyar Nijar ke watsi da kuma wulakanta dadaddiya kuma kyakkyawar alakar da ke tsakanin Nijeriya da Nijar, kai ka ce wani wasan kwaikwayo ne da wasu kwararru suka shirya.
Duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sha amsa gayyata daga Muhammadu Yusuf da sauran huldar diflomasiyyar da suka kulla da gwamnatin Issoufo ta Jamhuriyar Nijar, da kuma bayar da gudummawa ga kasar, akwai wasu ‘yan tsiraru a cikin gwamnatin Nijar da ke ganin cewa kokarin da Nijeriya ke yi wa kasar bai isa ba, kuma ba kamar yadda aka saba yi musu a baya ba daga bangaren shugabannin Nijeriya da suka gabata ba, musamman lokacin gwamnatin Jonathan.
Mu dauki misali yadda sauran gwamnatocin da suka gabata suka rika daukar tallafin a matsayin wata hanyar azurta kai, to a zamanin gwamnatin tsentsini ta Buhari ta tabbatar da cewa ana aikawa da wadannan kudade a inda ya kamata a tura su, ba tare da an yi aringizo ba.
Ko da ma a ce Buhari ya amince zai rika gabzar kudaden Nijeriya ya na bayarwa, to ba kamar gwamnatin da ta gabata a ke ciki yanzu ba. saboda babu ma kudaden da za a rika diba ana bayarwa tun daga hawan sa zuwa yau.
Abin takaici, an wayi gari a Nijar wasu ’yan ba-ni-na-iya cikin gwamnatin Issofou sun yi wa lamarin karkatattar fahimta, su na kallon kamar rowa yanzu Nijeriya ke yi wa kasar.
Dalili kenan suka dauko wani shirin yi wa shugaba mai Buhari mai neman sake fafata zaben 2019 da za a gudanar cikin Fabrairu 2019.
Wasu za su yi mamakin shin ya za a a ce kasa kamar Jamhuriyar Nijar da ke matukar amfana da Nijeriya, kuma ita ce ke kokarin kawo wa zaben Shugaba Buhari kafar-ungulu? To amsar mai sauki ce, amma kuma fuska uku gare ta:
Da farko dai su na ta kokarin sanyaya guyawun ‘yan Nijeriya masu saka jari a Nijar, wadanda ba su yi laifin tsaye ko na zaune ba, in banda harkokin hada-hadar su da suke yi a kasar.
An sha samun sa-toka-sa-katsi tsakanin wasu halastattun masu zuba jarin kasuwanci a Nijar da ke gudanar da ayyukan hadin-guiwa na manyan kwangiloli tare da gwamnatin kasar. Amma sai abu ya yi nisa, kafin a kai wajen kammalawa kowa ya ja ribar sa, sai gwamnatin Nijar ta waske, ta juyawa ‘yan Nijeriya baya, su kuma ‘yan kwangilar kasar su karasa ayyukan wadanda aka yi wa ‘yan Nijeriya kora-da-hali bayan da su aka fara.
Babban misali shi ne wani abin da ya faru da wani kamfanin kwangila na Nijeriya, mai suna Architeam Group Niaport SA, wanda shi wannan kamfanin an ba shi kwangilar fadada filin jirgin sama na Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar.
Shi wannan kamfani ya dukufa gudanar da aiki da gaskiya, saboda ya na da yakinin cewa Nijar ba za ta yi masa ‘yar-burum-burum ba. Har sai da ya antaya kuDin sa sama da dala milyan bakwai ya ta ayyuka.
Kwatsam, a rana Daya gwamnatin Mahamadou Issofou ta soke wannan kwangila ta maida kwangilar ga wani kamfanin da tun farko shi ta so ya gudanar da kwangilar.
Duk da cewa a cikin ka’idojin kwangilar an rattaba cewa idan kamfanin da ke gudanar da kwangila ya saba ka’ida ko lattin gama aiki, ko kuma jan-kafa, to za a gargade shi a rubuce har sau uku kafin a dauki mataki a kan sa. Abin takaici da kuma rashin adalci, Nijar ba ta gargadi wannan kamfani na Nijeriya ko sau daya ba.
Kuma yarjejeniya ta nuna cewa ko da an rubuta takardun gargadin sau uku, to idan soke kwangilar, zai kasance wani kamfani na Nijeriya ne aka bai wa aikin kwangilar. Amma babu daya daga cikin wadannan sharudda da aka gindaya da Jamguriyar Nijar ta yi aiki da su, kafin ta soke kwangilar aikin daga hannun Architeam Group na Nijeriya.
Alamomin nuna cin-fuska ga gwamnatin Nijar ke wa Gwamnatin Buhari ta Nijeriya a fili suke, domin duk da irin shiga tsakanin da Ma’aikatar Shari’a da ta Harkokin Waje na Nijeriya suka yi, bai shiga kunne Jamhuriyar Nijar ba.
Cikin watan Yuli an ce Buhari da kan sa ya shiga tsakani, inda ya roki gwamnatin Nijar da ta mutunta yarjejeniyar da ta kulla da kamfanin na Nijeriya. A nan shi da kan sa Shugaba Issofou ya nuna kamar ya gamsu da bayanan da Buhari ya yi masa, har ya nuna zai bi kadin batun yadda ya kamata. Amma maimakon haka, har wayewar garin yau tamkar bai ji kalaman da Buhari ya yi masa ba.
Karin abin takaicin kuma shi ne, wasu tsirarun cikin gwamnatin na kokarin ganin wasu ‘yan kasar masu rike da katin zaben Nijeriya sun shigo sun kada kuri’a domin su kayar da Buhari.
Wadannan batutuwa da al’amurra ne ya kamata a ce masu leken asirin Nijeriya sun tabbatar cewa bakin-haure da Jamhuriyar Nijar ko wata kasa ba su shigo sun dama wa kasar nan lissafi ba.
A duk lokacin da jami’an gwamnatin Nijar suka je kasashen da ba su da ofishin huldar diflomasiyya, Nijeriya ce ke daukar dawainiyar su a kasashen, saboda karimcin Nijeriya na sauke nauyin hakkin-makautaka da ke tsakanin ta da Nijar.
Cikin makon da ya gabata na saurari wani shiri da BBC ta yi a kan Boko Haram, inda na saurari wani babban mutum a Jamhuriyar Nijar ya na muzanta Nijeriya, har ya na cewa sojojin su sun fi na Nijeriya kwarewa da nuna jimirin a yaki da Boko Haram.
Shi wannan mutumin duk a wurin sa ba abin damuwa ba ne, dangane da irin tulin makaman da ‘yan bindigar da ke kashe mutane da yin garkuwa ke amfani da su a Jihar Zamfara da kuma Katsina cewa duk daga kan iyakar Nijeriya da Nijar ake shigo da su.
Lokaci ya yi da Nijeriya da kuma gwamnatin Buhari su daina daukar dawainiyar kananan kasashen da ke nuna mana halin kaza, wadda za ka ciyar da ita, sai dai bayan ta koshi ta goge baki, ba ta san ta ce ta gode ba. Kuma dama mu ma tunda gida bai gama koshi ba, sai mu daina bai wa jeji kenan.
A matsayin Jamhuriyar Nijar na kasa mai cikakken ’yanci, ta dade a matsayin kawar da Nijeriya ta kulla kyakkyawan zumunci da ita, ta yadda da wahala ma ka bambanta kasashen biyu idan aka yi la’akari da yadda auratayya ta shiga tsakani.
To idan har za a wayi gari wata gwamnati ta zo yanzu daga baya, ta nemi yi wa kasar nan kafar-ungulu, to Hausawa dai sun ce “Kunyar maras kunya, asara ce!”
Abubakar ya rubuto ne daga Abuja.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!