Connect with us

LABARAI

‘Yan Fansho Sun Roki el-Rufa’i, Ka Yi Wa Allah Ka Biya Mu Hakkinmu

Published

on

Sama da ‘yan fansho dubu 9 ne wadanda Gwamnan Jihar Kaduna ta sallama daga aikinsu suka gudanar da taron manema labarai, domin yin kira da kakkausar murya, ga Malam Nasiru Elrufai, da ya dubi Girman Allah, ya biyasu hakkokinsu.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun kungiyar, Ahmed Mu’azu, a yayin da yake zantawa da manema labarai a Sakatariyar ‘yan jaridu dake Kaduna.
Ahmed Mu’azu ya kara da bayyana cewa, “yau kimanin shekara daya da wasu watanni kenan, da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Elrufai, ta sallamemu mu akkala kusan dubu 9 da wasu ‘yan kai daga aiki, ba bisa ka’ida da laifin komai ba, sai domin son rai irin na siyasa.”
Ya kara da bayyana cewa, “ inaso na tabbatar maku da cewa, mu bama cikin Malaman Makaranta da aka kora daga aiki, kuma bama cikin Ma’aikatan Kananan hukumomin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta kora da aiki. Mu ma’aikata ne da muka fito daga fanni ma’aikatu daban daban dake fadin Jihar Kaduna. “
Ahmed Mu’azu, ya ci gaba da bayyana cewa, “ya zama wajibi mu fito mu bayyana ma duniya halin da muke ciki, musamman yadda Gwamnan Jihar Kaduna, a ko da yaushe ya kan fito karara a kafafen yada labarai ya na bayyana cewa, shi babu sauran wani ma’iakacin da aka sallama dake bin gwamnatin jihar bashi. Wannan magana da gwamna yake fadi, ba gaskiya bane, domin kullum gafara Sa muke gani, amma bamu ga Kaho ba.”
“Kasancewarmu masu bin doka da oda, munaso mu fito kara mu bayyana ma Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed Elrufai cewa, akwai sabani masu kama da juna akan maganar biyanmu hakkokinmu, kuma idan har akwai wani shaida guda daya wanda gwamna zai iya fitowa ya bayyana ma duniya cewa ga daya daga cikinmu wanda aka sallama daga aiki, kuma aka biyashi hakkokinsa. Muna kalubalantar Gwamnan, daya fito ya nuna ma duniya hakan. Duk abin da Gwamnan me tadi, ba gaskiya ba ne, kawai magana ce irin ta ‘yan siyasa.”
Daga karshe, ‘ya’yan kungiyar sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed Elrufai, da ta dubi girman allah, ta biyasu hakkokinsu, domin a cewarsu, mafi yawa daga cikinsu, halin kunci da bakin ciki, ya sanya sun fara rasa ransu. Wasu kuma na kwance a gadajen Asibiti.
uk kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Mai Magana da yawun Gwamnan Jihar Kaduna, Mista Samuel Aruwan, abin ya ci tura, domin wayoyinsa a kashe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!