Connect with us

LABARAI

‘Yan Majalisar Dokokin Bauchi Sun Samu Horo Kan Gudanar Da Shugabanci Ta Na’ura

Published

on

‘Yan majalisar dokoki na jihar Bauchi sun kammala samun horo akan tsarin gudanar da shugabanci ta hanyar na’ura mai kwakwalwa a cikin wani shirin taron bita na yini uku.
Taron bitar, wanda ya gudana a Kaduna tare da yin kira a garesu kan su yi amfani da darussan da suka koya ta hanyar da ta dace domin cimma muradun da aka sanya a gaba.
An shirya taron bitar ne domin kimantar da ‘yan majalisar a game da tsarin sadarwa na zamani da zummar inganta aiyukansu. An koyar da mahalarta taron yadda za su ci gajiyar tsarin gudanar da shugabanci ta hanyar na’ura mai kwakwalwa da kuma sauran fannoni da suka jibanci amfani da fasahar sadarwa ta zamani, hadi da yadda za a shawo kan kalubalen dake kunshe a cikin tsarin da zummar samar da nagartaccen shugabanci.
An kuma koyar da mambobin majalisar yadda za su kirkiri manufofi da dabaru da zasu shawo kan kalubalen da sabbin fasahohi na zamani.
Kazalika, an horar da ‘yan majalisar akan tsarin aiwatar da aiyukan shugabanci ta hanyar na’urar kwamfuta a cikin kasashe ‘yan rukuni na uku musammnan ma Nijeriya a bisa bukatar da take da ita ta cimma muhimman kayan more rayuwa.
A jawabin da yayi bayan bikin rufe taron bitar, Kakakin majalisar Dokoki na jihar Bauchi, Kawuwa Shehu Damina godiya yayi wa wadanda suka shirya taron bitar bisa yadda suka kimantar da ‘yan majalisar akan muhimman darussa da ake bukata, tare da bayyana jin dadinsa a game da muhimmanci da tsarin gudanar da shugabanci ta hanyar na’ura mai kwakwalwa yake da shi ga mambobin majalisar a game da aiyukansu, kana yayi alkawarin samar da kyakkyawan yanayi da zai baiwa ‘ya’yan majalisar damar kaiwa ga nasara.
Ya ce ‘yan majalisar sun samu ilimin da ake bukata wajen samar da abubuwan da ake marmarinsu a fannin jagoranci ta hanyar na’urar kwamfuta da zummar inganta kwazo da kuma tabbatar da gaskiya da adalci, da kuma irin aikin hadin gwuiwa da ake bukata domin tabbatar da cewar, gwamnati ta kai ga cimma nasarori akan dukkan manufofi da shirye-shiryen ta.
Sauran mahalarta taron bitar da suka yi magana a wajen bikin rufe taron karawa juna sanin, sun bayyana muhimmancin taron bitar ne musammnan ma irin ilimi da suka ce sun samu akan tsarin jagoranci na majalisar dokoki a fannin na’ura mai kwakwalwa, sun kuma yi alkawarin yin amfani da abubuwan da suka koya ta hanyar da ta dace domin inganta shugabanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!