Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yan Takarar Gwamnan Taraba Na PDP Da APC Sun Ki Sa Hannu

Published

on

Gwamnan Jihar Taraba, dan takaran Jam’iyyar PDP, Darius Ishaku, tsohuwar Ministar harkokin mata, ‘yar takarar Jam’iyyar UDP, Hajiya Aisha Alhassan, da dan takaran Jam’iyyar APC, Sani Danladi, sun ki halartar taron sanya hannu a bisa yarjejeniyar zaman lafiya da aka shirya a ranar Alhamis din nan.
An yi taron sanya hannun ne a shalkwatar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Taraba, da ke Jalingo.
Duk da cewa, manyan ‘yan takaran su uku ba su halarci bikin sa hannun ba, sauran ‘yan takaran 14 da suka hada da, Mista Kefas Sule, na Jam’iyyar ABP, duk sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyan.


Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Taraba, Mista Dabid Akinremi, wanda ya shugabanci bikin sanya hannu a kan yarjejeniyar, ya ce manufar sanya hannu a kan yarjejeniyar shi ne, daukan alkawari daga ‘yan takaran a kan za su gudanar da zaben a cikin lumana.
“A matsayin mu na kasa, ba za mu taba ci gaba ba, matukar ba mu habaka samar da zaman lafiya ba. Ina rokon ku, ku masu ruwa da tsaki a kan harkan zaben da ku guji tayar da hargitsi.

“In dai har ana tsayawa zabe ne domin a yi wa al’umma aiki, to ai babu bukatar tayar da rikici kafin, a lokacin ko kuma bayan zaben,” in ji shi.
Kwamishinan ya yi alkawarin ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su ba su cikakken kariya iri guda, kafin a lokacin da kuma ma bayan zaben, duk kuma da kiran da ya yi ga Jam’iyyun da su kintsa, amma su guji tayar da rikici.
Kwamishinan zabe na Jihar Taraba, Baba Yusuf, ya yi alkawarin hukumar zaben ta INEC, ta kuduri aniyar gudanar da zaben da kuma yi wa dukkanin Jam’iyyun adalci.


Da yake mayar da martani a madadin sauran ‘yan takaran, Mista Kefas Sule, na Jam’iyyar ABP, ya yi wa jami’an tsaron godiya a kan wannan shirin da suka yi na sanya a yi alkawarin warware duk wani sabani a tsakanin ‘yan takaran, da su kuma tsayu a kan alkawarin da suka sanya hannu a kansa.
Sule, ya yi kira ga sauran ‘yan takaran da ba su halarci bikin sanya hannu din ba, da su yi aniyar zuwa su sanya hannun na su a kan yarjejeniyar domin tabbatar da samar da zaman lafiya a lokacin zaben a Jihar ta Taraba.


Wakilinmu ya ba mu rahoton cewa, Gwamna Darius Ishaku da Sanata Aisha Alhassan, sun aiko ne da wakilansu, amma sai aka ki a amince masu, inda jami’an da ke wajen sa hannun suka dage a kan cewa tilas ne su zo su sanya hannun da kansu.
Amma shi dan takaran Jam’iyyar APC a Jihar, Sani Danladi, bai zo ba, bai kuma yiwo aike ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!